Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya ba da umarnin a gaggauta biyan albashi da fansho na watan Yuni ga ma’aikatan jihar da ‘yan fansho.
Wannan labari ya zo ne ta bakin Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Abubakar Bawa.
A cewarsa an yi hakan ne da nufin gudanar da bikin Sallah ba tare da damuwa ba.