Real Madrid ta miƙa tayin yuro miliyan 160 don sayen ɗan wasan gaba Kylian Mbappe daga Paris St-Germain.
Ɗan wasan mai shekara 22 da ya lashe Kofin Duniya, ya koma PSG a 2017 kan kuɗi da suka kai fan miliyan 165 wanda kuma yarjejeniyarsa za ta zo ƙarshe a Yunin 2022.
Mbappe ya ci wa PSG ƙwallo 133 cikin wasa 174 da ya buga mata, inda ya lashe kofin gasar Ligue 1 uku da French Cup uku.
Real Madrid wadda ake bi bashin da ya kai kusan fan biliyan ɗaya, David Alaba kaɗai ta ɗauka a wannan kakar daga Bayern Munich kuma kyauta.
Ganin cewa Sergio Ramos da Raphael Varane waɗanda ke ɗaukar albashi mai yawa sun bar ƙungiyar, Real na ganin za ta iya sayo Mbappe ba tare da matsalar kuɗi ba.
Sai dai babu cikakken bayani kan yadda za a tsara biyan kuɗin sannan kuma har yanzu PSG ba ta ce komai kan tayin ba tukunna.
(BBCHAUSA)