Kwamandan ISWAP Abu Sa’idu Ya Shiga Hannun Jami’an Tsaro

Dakarun  sojan Najeriya bataliya ta 144 dake rundunar Operation Haɗin Kai da aka girke a  Madagali a jihar Adamawa sun samu nasarar kama wani kwamanda a ƙungiyar ƴan ta’addar ISWAP, Sa’idu Hassan Lawan wanda aka fi sani da Abu Sa’idu.

Ƙasurgumin ɗan ta’addar na daga cikin jerin sunayen ƴan ta’addar da jami’an tsaro suke nema ruwa a jallo an kuma kama shi a wani  tarko da jami’an tsaro su kai masa a yankin  kasuwar Mubi a ranar 9 ga watan Maris.

Wata majiya dake jami’an tsaro sun faɗawa Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi cewa Sa’idu Hassan Yellow mai shekaru 32 shi ne wanda ya tsara farmakin da aka kai Askira Uba a ranar 21 ga watan Nuwamban 2021 inda aka kashe kwamandan birged ta 28 da kuma wasu sojoji uku.

More from this stream

Recomended