Kungiyoyin Premier shida sun hana ‘yan Brazil zuwa buga mata wasa

Premier League trophy

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyoyin Premier League shida sun hana ‘yan wasan Brazil zuwa buga wa tawagar wasannin shiga gasar kofin duniya a Satumba.

Tawagar Brazil za ta kara da ta Chile da Argentina da kuma ta Peru a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya.

Duk da barazanar da Fifa ta yi wa kungiyoyin cewar za ta ci tarar su, bai tsoratar da su ba, bayan da Birtaniya ta ayyana Brazil daya daga kashen da ke da hadarin kamuwa da cutar korona.

Kungiyoyin da suka hana ‘yan wasan Brazil zuwa buga wa kasar tamaula sun hada da Chelsea da Liverpool da Manchester City da Manchester United da Leeds United da kuma Everton.

Duk dan kwallon da ya je kasar da ke da hadarin kamuwa da cutar korona, idan ya koma Birtaniya sai ya killace kansa kwana 10, hakan wasu ba za su buga karawar uku ba kenan da zarar sun isa Ingila.

Hakan na nufin ‘yan kwallon ba za su buga wa kungiyoyin su wasa biyu a gasar Premier League da daya a Champions League a bana, wadanda suka bukaci gwamnati ta daga musu kafa ba sai sun killace kansu ba.

‘Yan wasan Brazil da abin ya shafa sun hada da Thiago Silva da Roberto Firmino da Fabinho da Alisson Becker da Ederson da Gabriel Jesus da Fred da Raphinha da kuma Richarlison.

Watakila hukumar kwallon kafa ta Brazil ta shigar da korafi ga Fifa, hakan zai sa hukumar kwallon kafa ta duniya ta iya dakatar da ‘yan kwallon daga buga wasa na kwana biyar

Tun farko shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Gianni Infantino ya bukaci gwamnatin Burtaniya da ta daga kafa ga ‘yan wasan da suka je buga wa kasashen su wasanni – cewar ba sai sun killace kan su ba idan suka koma Ingila.

More News

Ƴan Fashin Daji Sun Kashe Mutane 7 A Jihar Kebbi

Mutane 7 aka bada rahoton ƴan fashin daji sun kashe  a garin Tudun Bici dake ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi. A cewar mazauna...

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraÉ—iyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...