Kungiyar Likitoci Ta Nemi Gwamnatin Najeriya Ta Dakatar Da Aikin Rijistar Katin Zama Dan Kasa

Wannan kira ya biyo bayan yadda jama’a ke tururuwa kullum zuwa ofisoshin hukumar NIMC yin rajistar kafin zama dan kasa, ba tare da bin ka’idojin da aka gindaya na kare kai daga kamuwa da cutar coronavirus.

Shugaban kungiyar likitoci na kasa, Farfesa Innocent Ujah, ya ce bai ga wani dalili da zai sa gwamnati ta nemi a yi rajistar katin zama dan kasa yanzu ba, duba da yadda ake fama da annobar cutar coronavirus.

Farfesa Ujah, ya ce abin da ya kamata a yi shi ne a fuskanci yadda za a iya shawo kan cutar da ke ta kara bazuwa domin a yi kokarin dakile ta.

Amma ga babbar jami’a a hukumar zama dan kasa, Hajiya Hadiza Ali Dagabana, ta na ganin dakatar da aikin yin rijistar ba zai yi wa kasa kyau ba, domin a cewar ta akwai kwararan dalilai da suka sa aka fara yin rajistar tun shekarar 2015.

Hadiza Ali, ta ce ya zuwa yanzu suna da wadanda suka riga suka yi rajista har miliyan 44 a cikin rumbun su, kuma idan aka yi la’akari da yawan masu lambobin waya a kasa da suka kai miliyan 85, to yanzu ne aka kusan yi wa rabin su rajista.

Daya cikin matasan da suka je cibiyar domin yin rajista, Saidu Ibrahim, ya bayana ra’ayinsa cewa akwai alamun karancin ma’aikata a cibiyar shi ya sa ake dadewa ba a yi wa mutum rajista ba.

Saidu ya bada shawarar cewa kamata ya yi gwamnati ta yi saurin kai dauki ga hukumar wajen kara yawan ma’aikata.

Wanan batu na rajistar katin zama dan kasa na daukar hankalin yawacin hukumomin gwamnati domin a yanzu haka hukumar Kare Hadura ta kasa FRSC, karkashi jagorancin Boboye Oyeyemi, ta bada umurnin cewa nan da yan watanni mutum ba zai iya rajistar abin hawa ba sai da katin zama dan kasa.

(VOA Hausa)

More News

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...