Kungiyar CAN Ta Tabbatar Da Kama Mabiyanta

Shugaban kungiyar Kiristocin ta CAN a jIhar Kaduna Ravaran Joseph John Hayap ne ya yiwa manema labaru karin haske game da wannan batu.

Ravaran Hayap yace, baicin wasu da aka kashe, a cikin wannan dare ‘yan bindigar sun kama mutanen su goma sha takwas suka yi awon gaba da su. Yace sun ci gaba da tattaunawa da jami’an tsaro tun lokacin faruwar wannan ala’amari.

Shugaban Kristan na jihar Kaduna Ravaran Joseph John Hayap ya yi kira ga gwamnati ta yi abin da yakamata ta ceto musu mutanen su. Yace babban abin da ya dace gwamnati ta yi shine ta samar da tsaro mai inganci, saboda bai kamaci a ci gaba da kama mutane ana biya kudin fansa ba.

Sai dai rundunar yan-sandan jahar Kaduna ta musunta batun kisa a jihar Kaduna, sannan ta ce mutane goma sha biyar aka sace ba goma sha takwas da ake fadi ba ciki har da malamin addinin kiristan a wajen ibada a jiya lahadi.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jahar Kaduna DSP Yakubu Sabo ne ya tabbatar wa da Muryar Amurka wannan lamari. DSP Yakubu Sabo yace tuni aka tura runduna ta kwararrun jami’ai kuma suna nan suna aiki domin gano mutanen.

Ya zuwa yanzu dai yawan sace mutane a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ya dan lafa sai dai ana kara samun karuwar biyo mutane garuruwan su don sace su da nufin neman kudin fansa.

Related Articles