Kun san yawan mutanen da man fetur ya kashe a Najeriya? | BBC Hausa

hatsarin tankar mai

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Da sannu-sannu, fashewar butun man fetur da hadarin manyan motocin dakon mai na ci gaba da zama silar mutuwar ‘yan Najeriya.

Muhammad Kabir Abubakar, jami’i a hukumar kiyaye hadurra ta kasa, ya ce ‘yan Najeriya fiye da mutum 600 ne suka mutu a shekaru biyu da suka gabata sakamakon hadarin motocin dakon mai.

Ya ce mutum 302 ne suka mutu a 2018, inda mutum 308 suka mutu a shekara 2017 sakamakon hadurran motocin dakon mai.

Muhammad Kabir Abubakar ya danganta irin wannan hadari da dalilai guda uku kamar haka:

  • Aiki fiye da kima da ke sa direbobin kwashe kwanaki suna aiki ba tare da sun runtsa idanunsu ba
  • Shan kayan maye da na kara kuzari
  • Tukin ganganci

Jami’in hukumar ta hadari ya nuna irin yadda wasu mutanan da ba su ji ba su gani ba ke mutuwa sakamakon hadarin motocin, inda wuta ke tashi ta ci gidaje da mutane.

  • AFCON: Yi hasashen kasar da za ta yi nasara a gasar kofin Afirka
  • Gasar cin kofin Afirka ta 2019

A hannu guda kuma, fashwar bututun man fetur na daya daga cikin hanyoyin mutuwar mutane da salwantar dukiyoyinsu.

Hukumar Ba da agaji ta Red Cross ta ce akalla dai mutum 100 ne suka mutu a ranar Alhamis din nan sannan da dama suka jikkata sakamakon bindigar da wani bututun mai ya yi a wani kauye da ke kusa da birnin Legas.

Ga jadawalin yadda jama’a suke rasa ransu a fashewar bututun mai a fadin Najeriya da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya buga.

  • Yuli, 10 2000 – Mutum 250 sun mutu a garin Jesse na jihar Delta.
  • Yuli, 16 2000 – Mutum 100 sun mutu a garin Warri na jihar Delta.
  • Nuwamba 30, 2000 – Mutum 60 sun mutu a garin masunta na Ebute da ke kusa da Legas.
  • Yuni 19, 2003 – Mutum 125 sun mutu a wani kauye da ke arewacin birnin Umuahia na jihar Abia.
  • Satumba 17, 2004 – Gommai sun mutu a birnin Legas lokacin da barayin mai suka yi kokarin satar man daga bututun kamfanin NNPC.
  • Mayu 12, 2006 – Mutum 250 sun mutu a wani wurin shakatawa na Inagbe da ke wajen birnin Legas.
  • Disamba 26, 2006 – Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce ta samu gawar mutum 269 lokacin da wani bututu ya yi bindiga a yankin Abule Egba da ke Lagos.
  • Disamber 26, 2007 – Akalla mutum 45 fashewar bututu ta kashe a wajen Lagos.
  • Mayu 15, 2008 – Akalla mutum 100 sun mutu sannan da dama sun jikkata sakamakon fashewar bututun mai a Lagos.
Image caption

Ana alakanta taruwar jama’a a wurin wutar fetir da mutuwar yawa

Masana makamashi irin su Bala Zakka, wani mai zaman kansa a birnin Legas, na ganin dole gwamnati ta tashi tsaye wajen daukar matakin hana afkuwar fashewar bututun mai.

Ya ce sai an wayar wa da jama’a kai dangane da illar kusantar bututun mai da satar man.

To sai dai kuma ya ce ita gwamnati sai ta yi kokarin rage wa ‘yan kasar radadin talauci da ya ce yana taimaka wa wajen an giza mutanen kusantar bututun domin satar mai.

Irin haka ma na faruwa da mutane a garuruwan da motocin daukar man fetur ke faduwa, inda ‘yan garin ke zuwa da manufar dibar ganima al’amarin da yake janyo musu mutuwa.

Ko a ranar Litinin din nan sai da mutum 35 suka mutu sannan fiye da 50 suka jikkata a lokacin da wata tankar dakon mai ta fadi a titi a yankin jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa motar ta fadi ne a kusa da wasu shaguna yayin da take wucewa ta kauyen Ahumbe.

Mazauna kauyen sun yi ta rububin zuwa kwasar man fetur din, amma sai motar ta yi bindiga – al’amarin da ya janwo tashin gobara a ilahirin yankin.

More News

An sanar da zaman makoki na kwana biyar saboda mutuwar shugaban kasa a Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya sanar da zaman makoki na kwanaki biyar saboda rasuwar shugaban kasar Ibrahim Raisi...

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...