Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya sanar da zaman makoki na kwanaki biyar saboda rasuwar shugaban kasar Ibrahim Raisi wanda ya mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu.
Wani jirgin sama mai saukar ungulu dauke da Raisi ya gamu da abin da ministan harkokin cikin gida Ahmad Vahidi ya tabbatar da cewa “sauka ne mai wuya” a ranar Lahadi.
Kamfanin dillancin labaran Iran ya labarto cewa, tashar talabijin ta Press TV ta Iran ta bayar da rahoton cewa, lamarin ya afku ne a kusa da birnin Jolfa mai tazarar kilomita 600 daga arewa maso yammacin Tehran babban birnin kasar ta Iran.
Rahotanni sun ce jirage masu saukar ungulu uku na cikin ayarin, yayin da sauran biyun suka koma ba tare da wata matsala ba.