Kun san mazauna birnin da ke kukan wutar lantarki ta musu yawa? | BBC Hausa

Yadda taurari suke a sararin samaniya

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Taurarin subahana abin ban sha’awa

Garuruwa da birane da ke kusa da tafkin Geneva, babban birnin Switzerland sun kasance cikin duhu a wani mataki na fadakarwa da wayar da kan jama’a a kan muhimmancin sanin illar hasken fitulun lantarki.

An karkashe fitulun kan titi, sannan kuma aka shawarci mutane su ma su kashe kwayayen lantarki na gidajensu a lokacin.

Wadanda suka shirya wannan abu sun ce sakamakon ya kasance na mai ban sha’awa, yadda birnin ya kasance da duhu, a lokacin samaniya kuma ta kasance tarwal da ado na taurarin subahana, abin ba magana.

Daman tun ba yanzu ba ‘yan sama jannati a birnin na Geneva sun sha kokawa cewa ba sa iya hangen taurari a sararin samaniya saboda fitilun kan hanya da suka mamaye titunan kasar.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tutar kasar Switzerland

Masana a bangaren muhalli sun ce illar hasken wutar lantarkin na shafar dabbobi da shuke-shuke.

An bukaci mutanen kasar miliyan guda da ke zaune kusa da tafkin na Geneva da su saki jikinsu da wannan duhun da suka kasance a cikinsa a daren domin su ganewa idanuwansu yadda yanayin taurari ya ke da daddare a sararin samaniya.

Sai dai saboda dalilai na tsaro, ba a jefa birnin na Geneva gaba daya cikin duhun ba, sannan an bukaci masu tafiya a kafa da masu tafiya a kekuna da su sanya kayan da za a iya ganinsu a hanya don gudun kada a kade su da abin hawa ko su yi karo da juna.

More from this stream

Recomended