Kotun Koli Ta Tabbatar Da Zaɓen Gwamnan jihar Akwa Ibom

Kotun Koli ta tabbatar da Umo Eno a matsayin halastaccen zaɓaɓɓen gwamnan jihar Akwa Ibom.

Rukunin alkalan kotun su biyar ƙarƙashin jagorancin mai shari’a, Uwani Abba-Aji ta yi watsi da ɗaukaka ƙara daban-daban guda uku da jam’iyun APC da ɗantakararta, Akanimo Udofia, da YPP da ɗantararta Albert Bassey da kuma jam’iyar NNPP da ɗantararta John Udoedehe suka shigar gaban kotun.

Jagoririn lauyoyin masu shigar da kara sun janye karar ta su ne bayan da kotun ta nuna musu cewa ɗaukaka ƙarar ta su bashi da tushe balle makama.

Yan takarar sun shigar da zarge-zarge da yawa akan Eno ɗaya daga ciki shi ne cewa gwamnan ya miƙawa hukumar zaɓe ta INEC takardar kammala sakandare ta jabu.

Kotun ta nemi jin ba’asin ko masu ƙarar sun kira jami’an hukumar shiryawa jarrabawar WAEC domin su bayar da sheda kan ingancin takardar kammala makarantar.

A watan Satumba ne kotun sauraren kararrakin zabe ta tabbatar da nasarar da Eno ya samu.

Itama kotun ɗaukaka kara dake Lagos ƙarƙashin mai shari’a, Festus Obande ya tabbatar da hukuncin kotun sauraren kararrakin zaben.

More from this stream

Recomended