Kotun ɗaukaka ƙara dake Abuja ta tabbatar da Julius Abure a matsayin halastaccen shugaban jam’iyar Labour Party na ƙasa.
A ranar Laraba kotun ɗaukaka ƙarar ta jingine hukuncin babbar kotun birnin tarayya Abuja da ya hana Abure da wasu mutane biyu ayyana kansu a matsayin masu jagorantar jam’iyar a ƙasa baki daya.
Mai shari’a Hamman Barka da ya jagoranci alƙalai uku da suka yanke hukuncin ya ce babbar kotun birnin tarayya Abuja tayi kuskure da tayi tunanin cewa tana da hurumin sauraren ƙarar.
Kotun ta kuma bayar da umarnin masu ƙara su biya Abure da sauran mutane biyun da suka daukaka kara naira miliyan ɗaya.
A cikin watan Afrilun shekarar 2023 ne babbar kotun birnin tarayya Abuja ta bada umarni da Abure ya daina ayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyar LP.
Kotun ƙarƙashin mai shari’a, Hamza Muazu ta kuma hana Faruk Ibrahim sakataren jam’iyar na ƙasa da Clement Ojukwu sakataren tsare-tsaren jam’iyar na ƙasa daga ayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyar.