Babbar kotun tarayya da ke Legas a ranar Juma’a ta tura , Idris Okuneye, wanda aka fi sani da Bobrisky gidan yari saboda wulakanta naira.
Mai shari’a Abimbola Awogboro ya yanke masa hukunci bayan ya yi nazari kan gaskiyar lamarin.
Bobrisky ya shaida wa kotun cewa bai san da dokar cin zarafin Naira ba.
Ya ce shi mai tasiri ne a shafukan sada zumunta mai mabiya sama da miliyan biyar.
Sai alkali ya gaya masa cewa rashin sanin doka ba uzuri ba ne.
Sai dai ya ce “Ba zan sake maimaita hakan ba ba. Na yi nadama.”
Tun da farko dai, an gurfanar da Bobrisky a kan tuhume-tuhume hudu na cin zarafin Naira da Hukumar EFCC ta yi masa.