Kotu ta saki ‘yan Shi’a 100 a Kaduna

An kama su ne bayan harin da dakarun rundunar sojin kasar suka kai musu a Zaria

An kama su ne bayan harin da dakarun rundunar sojin kasar suka kai musu a Zaria a 2015

Wata babbar kotu a jihar Kaduna ta saki ‘yan Kungiyar Harkar Islamiyya a Najeriya, mabiya Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Sanarwar da mai magana da yawun kungiyar, Ibrahim Musa, ya aike wa manema labarai ranar Juma’a ta ce mambobin kungiyar da kotun ta saka su ne kashin karshe da aka saka tun da aka kama su a 2015.

An kama su ne bayan harin da dakarun rundunar sojin kasar suka kai musu a Zaria, lamarin da ya yi sanadin mutuwar fiye da ‘yan Shi’a 300, a cewar kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch.

“Wannan ya kawo karshen shari’ar shekara hudu da muke yi, inda gwamnatin Kaduna ta kai karar mambobin Islamic Movement kusan 200 bayan sojin Najeriya sun kai musu hari a watan Disambar 2015, lamarin da ya kai da kisan fiye da mutum dubu da kuma binne su a wani katon kabari a asirce,” in ji Ibrahim Musa.

Ya kara da cewa sakin da aka yi wa ‘yan kungiyar ya wanke mambobinta da ma shugabanninta daga dukkan zargin da ya kai ga kisan da soji suka yi wa takwarorinsu a Zaria.

Har yanzu shugaban kungiyar, Sheikh El-Zakzaky da mai dakinsa na ci gaba da tsare a hannun hukumomin tsaron kasar, duk da umarnin sakinsu da kotuna daban-daban suka yi.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta sake su ba saboda ta daukaka kara.

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...