Wata babbar kotun tarayya dake jihar Kano ta bayar da umarnin kamawa tare da bincike da kuma gurfanar da shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas.
Mahmoud Lamido shi ne ya shigar da kara gaban kotun inda ya zargi shugaban jam’iyyar da yin barazana ga rayuwarsa, tayar da zaune tsaye da kuma yin kalaman tayar da jarirai.
Lauyan Lamido ya fadawa kotun cewa Abbas ya yi barazanar kashe mutumin da yake karewa a wata waya da suka yi.
Alkalin kotun mai shari’a S.A Amobeda ya dage sauraron shari’ar ya zuwa ranar 16 ga watan Faburairu.