Kotu ta bayar da belin likitan da ake zargi da cirewa wata mata koɗa a Jos

Wata kotun majistire dake zamanta a Jos ta bayar da belin Noa Kekere mutumin da ake zargi da sace koɗar wata mata a garin Jos.

Yan sanda sun kama Kekere tare da wasu mutane biyu da suka taimaka masa wajen cire koɗar mutane biyu a Asibitin Murna Clinic and Maternity dake Ƴanshanu a karamar hukumar Jos North.

A yayin zaman shari’ar ranar Talata mai shari’a, Chief Majistire Joseph Chollom ya bayar da belin wanda ake zargi tare da gindaya wasu sharuɗa da suka haɗa mutane biyu da za su tsaya masa da suke da cikakkun takardar mallakar gida da kuma basaraken gargajiya guda ɗaya.

More News

NFF ta naɗa Finidi George a matsayin sabon kocin Super Eagle

An naɗa Finidi George a matsayin sabon mai horar da kungiyar ƙwallon ƙafar Najeriya wato Super Eagle. Hukumar ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, NFF ita ta...

Gwamnan Edo Zai Fara Biyan 70,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya sanar da mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan ga ma'aikatan jihar inda za a riƙa biyan naira dubu 70,000. Gwamnan...

JAMB ta fitar da sakamakon jarabawar 2024

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB, ta fitar da sakamakon jarrabawar shekarar 2024, watau sakamakon UTME.Sama da mutane miliyan 1.94...

Ortom ya shawarci Yahaya Bello da ya miƙa kansa ga EFCC

Tsohom gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom, a ranar Lahadin da ta gabata, ya bukaci takwaransa na jihar Kogi, Yahaya Bello, da ya fito daga...