JAMB ta fitar da sakamakon jarabawar 2024

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB, ta fitar da sakamakon jarrabawar shekarar 2024, watau sakamakon UTME.

Sama da mutane miliyan 1.94 ne suka yi rajista tare da zana jarrabawar a garuruwa 118 da cibiyoyi sama da 700 a fadin kasar nan.

Magatakardar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya sanar da fitar da sakamakon a wani taron manema labarai da ya gudanar a hedikwatar hukumar, Bwari, a Abuja a ranar Litinin.

Jarrabawar da ta fara a ranar Juma’a, 19 ga Afrilu ta ƙare ne a ranar Litinin, 29 ga Afrilu, 2024.

More from this stream

Recomended