Kotu ta bayar da belin Emefiele bayan ya cika sharuÉ—a

Kotu ta bayar da belin tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele bayan da ya cika dukkanin sharudan beli da kotun ta gindaya.

Emefiele wanda ya isa harabar Babbar Kotun Lagos bisa rakiyar jami’an hukumar EFCC  ranar Juma’a ya samu damar tafiya gidansa bayan kammala zaman kotun.

Alƙali Rahman Oshodi wanda ya yanke hukunci kan batun belin ya bayar da belin Emefiele kan kuɗi naira miliyan ₦50 da kuma wasu mutane biyu da za a su tsaya masa kan kuɗi makamancin haka.

Jim ƙadan bayan da aka bayar da belin sai kotun ta shiga sauraron ƙarar da EFCC ta shigar inda lauyoyin masu ƙara suka gabatar da sheda ba farko.

Shedar farko, Monday Osazuwa wanda ma’aikaci ne a CBN ya faÉ—awa kotun cewa a lokuta da dama tsohon gwamnan babban bankin na CBN ya tura shi ya karbo kuÉ—i dalar Amurka miliyan 3.

More News

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...

NFF ta naÉ—a Finidi George a matsayin sabon kocin Super Eagle

An naɗa Finidi George a matsayin sabon mai horar da kungiyar ƙwallon ƙafar Najeriya wato Super Eagle. Hukumar ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, NFF ita ta...

Gwamnan Edo Zai Fara Biyan 70,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya sanar da mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan ga ma'aikatan jihar inda za a riƙa biyan naira dubu 70,000. Gwamnan...

JAMB ta fitar da sakamakon jarabawar 2024

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB, ta fitar da sakamakon jarrabawar shekarar 2024, watau sakamakon UTME.Sama da mutane miliyan 1.94...