Kotu ta ɗaure wasu ƴan damfara a Kano

Wata babbar kotun jihar Kano karkashin mai shari’a Ibrahim Musa Karaye ta yanke wa wasu ‘yan damfara biyu, Benjamin Okechukwu Udeagwu da Benjamin Amos Olamide hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari bisa samun su da laifin da suka shafi damfara a yanar gizo.

An daure su ne bayan sun amsa laifuka guda daya da suka shafi zamba a yanar gizo bayan da rundunar shiyyar Kano ta EFCC ta gurfanar da su a gaban kuliya.

Takardar laifin da ake tuhumar Udeagwu cewa ta yi: “Kai, Benjamin Okechukwu Udeagwu a wani lokaci a cikin watan Satumba, 2023 a Kano da ke karkashin hurumin babbar kotun Kano, da niyyar zamba, ya samu dala $50 ta hanyar zamba a matsayin Brad George dan kasar Amurka wanda ke nuna cewa kun san karya ne kuma kuka aikata laifin damfara ta hanyar da ta saɓa wa sashe na 321 na dokar Penal Code”

More from this stream

Recomended