Kotu ta ɗaure mutumin sa ya yi sama-da-faɗi da kuɗin marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda samunsa da laifin wawure kuɗin marayu kimanin naira miliyan 12.

Hukumar EFCC ce ta wallafa bayanin ranar Talata shafinta na Twitter.

Tun a ranar 3 ga watan Yulin 2023 ne hukumar EFCC ta gurfanar da shi a gaban kotun kan zargin karkatar da dukiyoyin magada da aka ƙiyasta kuɗinsu ya kai kimanin naira miliyan 12 ga buƙatar kansa maimakon amfani da ita wajen kula da magada.

Dukiyoyin sun haɗa da gidaje uku da filaye biyu da aka kange – ɗaya daga ciki ɗauke da shaguna bakwai sai gidajen burodi biyu da wani fili da manyan tankoki biyu sai babban injin janareto.

More from this stream

Recomended