(Kiwon lafiya): Ko kun san hanyoyin kare kai daga cutar hawan jini?

Yadda ake gwada hawan jini

Hakkin mallakar hoto
Healthline

Masana kiwon lafiya a Najeriya, sun yi karin haske a kan matakan da suka da ce abi domin kaucewa kamuwa da cutar hawan jini wato Hypertension a turance.

Daga cikin abubuwan akwai motsa jiki da daina cin abincin gongoni irin na turawa saboda akwai gishiri da yawa a cikinsu, sannan akwai cin abinci mai gina jiki.

Dr Bashir Mijinyawa, likita ne da ke Abuja babban birnin Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, baya ga wadannan abubuwa na sama, akwai kuma bukatar mutane su rinka samun isashshen hutu da barci da kuma rage damuwa.

Likitan ya ce, yanzu masu cutar hawan jini a Najeriya na kara yawa, domin akwai binciken da aka yi wanda ya nuna cewa a cikin mutum 100, a kan samu mutum 10 na da wannan cuta.

Dr Mijinyawa, ya ce ba a fiye warkewa dga wannan cuta ba, sai dai wanda ya ke da ita ya rinka shan magani kusan koda yaushe musamman ma wadanda suka gaji cutar.

Kazalika likitan ya ce, yawancin masu dauke da wannan cuta ta hawan jini a wasu lokutan ta kan bata musu zuciya ko koda ko kuma ta janyo musu shanyewar rabin jiki.

Ya ce a wasu lokutan ma hawan jini kan bata hanyoyin jini.

Likitan ya ce, bisa la’akari da illolin da wannan cuta kan haifar, yana da kyau mutane su rinka zuwa asibiti domin a duba su a kai- a kai musamman wadanda suka san sun gada ko kuma masu kiba.

Cutar hawan jini dai babbar cuta ce da ke addabar al’ummar duniya, kuma ba manya kadai ta ke kamawa ba, hatta yara ma su kan kamu da cutar.

Muhimmancin cutar ne ya sa aka kebe kowacce ranar 17 ga watan Mayu domin gudanar da bikin zagayowar ranar a fadin duniya ta yadda za a fadakar da jama’a a kan irin illolinta da ma hanyoyin da za a bi wajen kare kamuwa da ita.

Taken ranar ta wannan shekara dai ita ce ku san yawanku wato ” Know Your Numbers” ke nan a turance.

More News

An ƙona sakatariyar ƙananan hukumomi 2 a jihar Rivers

Wasu da ake kyautata zaton ɓatagari ne sun ƙona wani sashe na sakatariyar ƙananan hukumomin Eleme da Ikwerre dake jihar Rivers. Ƙona ginin na zuwa...

Ƴanbindiga sun hallaka wani shugaban APC a Kebbi

Wasu ‘yan bindiga sun harbe Bako Bala, shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Suru a jihar Kebbi, a yayin wani yunkurin yin garkuwa da...

Kotu ta hana VIO kamawa, tsare motoci ko cin tarar direbobi a kan hanya

Justis Evelyn Maha ta Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta bayar da umarni da ya hana Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa, wanda aka...

Sojojin Najeriya sun hallaka masu haramtacciyar harƙar man fetur

Dakarun runduna ta 6 ta sojojin Najeriya sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin barayin man fetur ne, tare da cafke wasu 18...