Matakin shugaba Buhari na ƙin sanya hannu kan kuɗirin dokar zaɓe da majalisar dokoki ta amince na ci gaba da haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya.
Batun zaɓen ƴar tinke ne ya fi jan hankali a kuɗirin dokar, kuma Shugaban ya bayyana dalilansa na ƙin sanya hannu, a wasiƙar da ya rubutawa majalisa, inda ya ce zaben ‘yar tinke zai lakume kuɗi da kuma bayyana fargabar ƙalubalen tsaro wurin gudanar da shi.
Sai dai wannan matakin ya haifar da mahawara a shafukan sada zumunta inda wasu ke goyon bayan shugaban, wasu ƴan ƙasar da ƙungiyoyin fararen hula kuma ke sukar matakin tare da yin kira ga majalisa ta yi gaban kanta ta amince da kuɗirin ko da shugaban ya ƙi sa hannu.
Tuni Majalisar dokokin kasar ta amince da dokar da ta ƙunshi amincewa da batun zaɓen fid da gwani ta hanyar ƴar tinƙe wanda aka fi sani da ƙato bayan ƙato. Kuma dama shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kawai ake jira ya sanya hannu a kuɗirin domin ya zama doka, kuma yanzu ya ƙi sanya hannu.
Buhari da majalisar tarayyar Najeriya na cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a shafukan sada zumunta musamman a Twitter a ranar Talata.
Ƙungiyoyin fararen hula da kare haƙƙin ɗan Adam kamar CISLAC a cikin wata sanarwa ta buƙaci majalisar tarayya ta hau kujerar naki ta ƙi amincewa da matakin shugaban game da batun dokar zaɓen.
Amma batun ya janyo mahawara kan ikon da majalisa take da shi na yin watsi da matakin shugaban.
Abin da ƴan Najeriya ke cewa:
Ƴan Najeriya da dama na bayyana ra’ayoyi ne mabanbamta, inda wasu ke bayyana goyon bayan dalilan shugaba Buhari wasu kuma na ganin matakin kin amincewa da sabon tsarin zaɓen kamar tsohe wa mutane shiga zaɓuka ne a duka matakai.