A daren Asabar din ta gabata ne, ‘yan bindiga dauke da manyan bindigogi suka harbi Maigarin Yandaka, da ke cikin Karamar Hukumar Batsari, Alhaji Shehu Iliyasu. Inda suka harbe shi a tsakiyar kansa da kuma hannunsa. Kuma suka sace matarsa da ‘ya’yansa guda uku suka tafi da su.
An yi gaggawar kai shi asibitin Katsina, domin cire masa harsashen dake cikin kansa da hannu, inda aka wuce da shi asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, yanzu haka yana can kwance.
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, ta tabbatar da afkuwar wannan hari da aka kai garin Yandaka, dake cikin karamar hukumar Batsari ta bakin mai magana da yawun rundunar SP Gambo Isa.