Kasuwar ‘yan kwalllon kafa: Makomar Kane, Ronaldo, Varane, Aguero, Bailly, Martinez

Harry Kane

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,
Harry Kane ba ya son barin Premier

Dan wasan gaba na Ingila Harry Kane, mai shekara 27, na son ci gaba da zama a gasar Premier, inda zai tafi Manchester United ko kuma Manchester City idan har zai bar Tottenham. (Jaridar Independent)

Manchester United na son sake sayen tsohon dan wasanta na gaba Cristiano Ronaldo, mai shekara 36, daga Juventus kuma kungiyar ta ce za ta iya yarda su yi musaya da dan wasan tsakiya na Faransa Paul Pogba, mai shekara 28. (Jaridar Calciomercato)

Haka kuma Manchester United din na son sayen dan wasan baya na Real Madrid kuma da Faransa Raphael Varane. Real ta yi wa dan wasan mai shekara 27 farashin fam miliyan 60. (Jaridar Mail)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,
Manchester United ta ce Paul Pogba ba ya jin dadin zamansa a kungiyar

United da Chelsea na son sayen dan wasan gaba na Juventus da kuma Argentina Paulo Dybala, mai shekara 27. (Jaridar Tuttosport)

Kungiyar Tottenham na ganin kociyan Wolves Nuno Espirito Santo ka iya zama wanda ya fi dacewa yam aye gurbin Jose Mourinho. (Jaridar Express)

Har yanzu Chelsea na sha’awar dan wasan baya na Uruguay da Atletico Madrid Jose Maria Gimenez, mai shekara 26, amma kuma idan so samu ne kungiyar ta fi son dan Sevilla na tawagar Faransa ta ‘yan kasa da shekara 21, Jules Kounde mai shekara 22. (Jaridar La Razon ta Sifaniya)

Real Madrid na da kwarin guiwa har yanzu na sayen dan wasan gaba na Faransa Kylian Mbappe a bazaran nan, amma kuma ta iya yuwuwa dan wasan mai shekara 22 ya ci gaba da zama a Paris St-Germain. (Jaridar Goal)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Manchester United na son dawo da tsohon dan wasanta Cristiano Ronaldo

Barcelona za ta yi wa dan wasan Manchester City na gaba Sergio Aguero, mai shekara 32, tayin daukarsa a bazaran nan, amma dai ba za ta bas hi albashin fam miliyan 8.7 a shekara da Juventus ta yi masa tayi ba. (Jaridar Sport)

Tottenham na duba yuwuwar sayen dan wasan gaba na Austria Sasa Kalajdzic, mai shekara 23, wanda ke wasa a Stuttgart. (Jaridar Eurosport)

Boca Juniors na son daukar dan wasan tsakiya na Arsenal Lucas Torreira. Dan wasan da ke taka wa kasarsa Uruguay leda mai shekara 25 a yanzu yana zaman aro a Atletico Madrid, wadda ita kuma ba ta son daukarsa ya zaman a dindindin a Sifaniyar. (Jaridar TyC Sports ta Sifaniya)

Dan wasan baya na Ivory Coast Eric Bailly, mai shekara 27, ba zai sabunta zamansa a Manchester United ba, a bazaran na, domin yana son sauya sheka, bayan kwantiraginsa yak are a karshen kakar nan. (Jaridar ESPN)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Eric Bailly na son tafiya daga Manchester United a bana

Aston Villa za ta samu babban tayi na mai tsaron ragarta Emiliano Martinez a bazaran nan. Rahotanni na cewa Manchester United na harin dan kasar Argentina mai shekara 28. (Jaridar Football Insider)

Valencia ta nemi bayar da dan wasanta na gefe Goncalo Guedes, dan Portugal mai shekara 24, ga kungiyar Wolves. (Jaridar Mail)

Shi kuma dan wasan baya na kungiyar ta Wolves dan Portugal Ruben Vinagre, Benfica c eke harinsa. Dan wasan mai shekara 22 a yanzu yana zaman aro a Famalicao. (Jaridar Football Insider)

More News

Ƴan Fashin Daji Sun Kashe Mutane 7 A Jihar Kebbi

Mutane 7 aka bada rahoton ƴan fashin daji sun kashe  a garin Tudun Bici dake ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi. A cewar mazauna...

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraÉ—iyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...