Kasuwar ‘yan ƙwallon ƙafa: Newcastle za ta ɗauko Coutinho, Liverpool na zawarcin Koulibaly

Newcastle za ta kashe euro 80m domin dauko dan wasan Barcelona da Brazil Philippe Coutinho idan shirinsu na son dauko shi ya tafi yadda ya kamata. Yanzu haka dan wasan mai shekara 27 yana zaman aro a Bayern Munich. (Mundo Deportivo – in Spanish)

Kazalika mutanen da za su sayi kungiyar ta Newcastle suna son dauko dan wasan Napoli da Senegal Kalidou Koulibaly. Ana sa ran kungiyar ta Italiya za ta sayar dan kwallon mai shekara 28 a kan £69.8m. (Sky Sports via Star)

A wani gefe kuma, Koulibaly yana duba yiwuwar komawa Liverpool.(Calciomercato – in Italian)

Borussia Dortmund tana cike da kwarin gwiwar cewa dan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, zai ci gaba da zama a kungiyar duk da rahotannin da ke cewa Manchester United za ta dauko shi. (Sky Sports)

Mai yiwuwa a bai wa Arsenal damar dauko dan wasan Inter Milan Mauro Icardi, mai shekara 27, domin maye gurbin dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang. Kwangilar Aubameyang, mai shekara 30, za ta kare a kakar wasa mai zuwa, yayin da shi kuma dan kasar Argentina Icardi yake zaman aro a Paris St-Germain. (Tuttosport via Teamtalk)

Arsenal na daf da kammala yarjejeniya ta dauko George Lewis. A baya dai dan kasar ta Norway, mai shekara 19, yana murza leda a Tromso. (Metro via Goal)

Matashin dan wasan Barcelona Marc Jurado, mai shekara 16, ya yi watsi da tayin da kungiyar ta yi masa na sanya hannu kan yarjejeniyar ci gaba da zama a can. Ana sa san dan wasan zai koma Manchester United a bazara. (ESPN)

Har yanzu dan wasan da Chelsea take son daukowa Dries Mertens bai amince ya tsawaita zamansa a Napoli ba. Kwangilar dan wasan na Belgium, mai shekara 33, za ta kare a bazara.(Calciomercato – in Italian)

Chelsea, Manchester United da kuma Tottenham suna zawarcin dan wasan tsakiya na Lazio Sergej Milinkovic-Savic. Za a kyale dan wasan na Serbia, mai shekara 25, ya bar kungiyar a kan £80m, a cewar jaridar (Mail)

Jaridar (Standard ta ambato shugaban tawagar kwallon kafar Kosovo yana cewa Liverpool tana son karbo aron dan wasan Kosovo da Wolfsburg, Milot Rashica, mai shekara 23

Leeds United ce take kan gaba a kungiyoyin da ke son dauko dan wasan Linfield Charlie Allen. Kungiyoyin Chelsea, Tottenham da Liverpool suna son dauko dan kasar ta Arewacin Ireland, mai shekara 17, a cewar jaridar(Yorkshire Post).

Chelsea na sha’awar sayen dan wasan Monaco Fode Ballo Toure. Kwangilar dan wasan na Faransa, mai shekara 23, ba za ta kare ba sai shekarar 2023. (Foot Mercato – in French)

(Express ta ambato wakilin Henrikh Mkhitaryan yana musanta cewa Arsenal tana son sayar da dan kwallon kafar ta Armenia. Mino Raiola ya ce batun da ake yadawa kan yiwuwar sayar da dan wasan mai shekara 31 “labarin karya” ne.

Dan wasan Barcelona dan kasar Croatia Ivan Rakitic, mai shekara 32, ya ce ba ya tunanin barin kungiyar duk da yake kwangilarsa za ta kare a 2021. (Sky Germany – in German)

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa ɗaya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faɗa tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...