Kasuwar musayar ‘yan ƙwallon ƙafa: Makomar Coutinho, Willian, Haaland, Sancho, Pochettino, Kavertz

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Chelsea, Manchester United da kuma Leicester sun tuntubi wakilin dan wasan Barcelona Philippe Coutinho domin dauko shi a bazara, sai dai dan wasan na Brazil dan shekara 27 ya fi son komawa Chelsea. (Sun)

Dan wasanChelsea dan kasar Brazil Willian, mai shekara 31, ya nuna alamar cewa zai iya sanya hannu a kan yarjejeniya ta takaitaccen lokaci zuwa karshen kakar wasa ta bana a yayin da ake sa ran kakar wasan Premier za ta zarta ranar 30 ga watan Yuni, wato ranar da kwangilarsa za ta kare. (Mail)

Tsohon dan wasan Liverpool John Barnes ya ce dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Norway Erling Braut Haaland, dan shekara 19, yana da dukkan kwarewar da ta kamata wajen maye gurbin Roberto Firmino a Anfield. (Express)

An tabbatarwa kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer cewa kungiyar za ta fafata sosai a kasuwar musayar ‘yan kwallon kafa a bazara bayan kungiyar ta bayyana cewa ta yi asarar £28m sakamakon annobar cutar korona. (Express)

Bayern Munich ta matsa kaimi a yunkurinta na dauko Jadon Sancho kafin a dakatar da kakar wasan bana sabda annobar korona, amma Borussia Dortmund, wadda take da kwarin gwiwa za a biya ta £100m kan dan wasan mai shekara 20, ba za ta sayar da shi ga abokan hamayyarta na Bundesliga ba. (Metro)

Tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya kammala hutun da ya dauka kuma ya ce yana fatan samun “aikin da ya dace”, a yayin da ake rade radin zai koma Newcastle. (Express)

Tsohon dan wasan United da Tottenham Dimitar Berbatov ya gargadi dan wasanBayer Leverkusen dan shekara 20 Kai Havertz, wanda ake rade radin zai koma Liverpool, Manchester United ko Chelsea, da ya guji komawa Gasar Premier. (Evening Standard)

Chelsea tana sha’awar dauko dan wasan Barcelona dan shekara 18 dan kasar Netherlands Xavier Mbuyamba a yayin da suke son dauko matasan ‘yan wasa saboda tasirin da annobar korona ta yi a kan harkokin kudin shigarsu. (Evening Standard)

Yunkurin daChelsea take yi na dauko gola ya gamu da cikas saboda golan Jamus Marc-Andre ter Stegen, mai shekara 28, yana shirin sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar shekara biyar a Barcelona. (Sun)

More News

Sojan Jamhuriyar Nijar sun kama Gawurtaccen Ɗan Fashin dajin Najeriya Kachalla Mai Daji

Dakarun sojan Jamhuriyar Nijar sun samu nasara kama gawurtaccen ɗan fashin dajin nan mai suna Kachalla Mai Daji a garin Illela dake kan iyakar...

Ƴan Fashin Daji Sun Kashe Mutane 7 A Jihar Kebbi

Mutane 7 aka bada rahoton ƴan fashin daji sun kashe  a garin Tudun Bici dake ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi. A cewar mazauna...

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraɗiyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...