Kasashen yammacin Afirka za su daina amfani da kudin CFA badi | BBC Hausa

Shugaba Macron da Alassane Ouattara na Cote d'Ivoire

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, da takwaransa Alassane Ouattara na Cote d’Ivoire sun sanar da matakin kirkirar kudin bai-daya na kasashen yammacin Afrika wanda zai kawo karshen yin amfani da kudin CFA na Faransa.

A wata ziyara da ya kai birnin Abidjan na Cote d’Ivoire Mista Macron ya ce kasashen yammacin Afirka sun dauki CFA wacce aka samar a 1945 a matsayin wata alama ta ci gaba da mulkin mallaka. Wanda suka ga ya dace su samar da sabon kudi na Eco da za a fara amfani da shi 2020.

Kasashe takwas na yammacin Afirka ne ke amfani da kudin CFA da suka hada da Benin da Burkina Faso da Guinea-Bissau da Ivory Coast da Mali da Nijar da Senegal da Togo da kuma Kamaru inda kuma za su dakatar da amfani da kudin na Faransa zuwa wanda za su samar.

An dauki lokaci kasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka a yammacin Afirka na tattauna yadda za su samar da kudin bai-daya kamar irin tsarin na Tarayyar Turai.

Ko a taron shugabannin kasashen Ecowas da aka gudanar a Abuja ranar asabar an sake tattauna batun tabbatar da sabon kudin da ake fatan fara amfani da shi a a badi.

Ana ganin sabon tsarin kudin zai habaka tattalin arzikin kasashen na yammacin Afirka.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Amma Wasu masana tattalin arziki kuma na ganin yanayin kasuwancin bai-daya a irin yanki na Afirka babban jan aiki ne, musamman shakku da ake nunawa game da sharudda da tabbatarwa da kuma cimma bukatun tattalin arziki a cikin lokaci wajen kafuwar wannan bukata ta su.

Irin wannan bukatar dai ta dauki kungiyar Tarayyar Turai shekaru da dama.

Masana na ganin ga dorewar tsarin, dole sai ya kasance an gudanar da mafi yawancin kasuwancin tsakanin kasashen na Afirka.

Masharhantan na ganin wannan shi ne babban kalubalen da za a fuskanta, domin yawancin kasashen Afirka sun fi hulda ne da kasashen waje maimakon makwabtansu na nahiyar.

Kasuwanci tsakanin kasashen Afirka bai wuce kashi 16 ba duka. A tsakaninsu da kasashen yankin Asiya kuma kashi 51, a Turai kuma adadin ya kai kashi 70.

Hakan ya nuna sabon kudin da kuma niyyar kasuwancin na bai-daya zai iya fuskantar kalubale kafin ya karbu cikin lokaci kankani.

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...