Kungiyar kamfanonin da suke da lasisin samar da kamfanonin sadarwa a Najeriya(ALTON) ta ce kuɗin da ake cajin masu amfani da wayar salula a yanzu ba abu ne da zai dore ba a halin da ake ciki yanzu.
Shugaban kungiyar Gbenga Adebayo shi ne ya bayyana haka a wurin taron masu ruwa da tsaki a harkar sadarwa da shugaban hukumar sadarwa ta kasa NCC, Dr Aminu Maida.
Ya ce ya kamata a duba farashin dai-dai yadda ake samun karuwar kuɗin da suke kashewa wajen gudanar da ayyukansu inda ya kara da cewa masu kamfanonin andora musu nauyin biyan haraji har kusan guda 52.