Kaduna: An kubutar da babban dan sanda daga hannun masu satar mutane

Wani dan sandan Najeriya

Image caption

‘Yan sanda a jihar Kaduna, Najeriya, sun ce an yi nasarar kubutar da babban jami’in dan sandan nan da aka sace, ACP I. Musa, mai lakabin Rambo, a kan hanyar Kaduna zuwa Jos a karshen mako.

Mai magana da yawun rundunar DSP Yakubu Sabo ya ce an kubutar da babban dan sandan ne tare da direbansa ba tare da ko rauni ba.

Sai dai a tattaunawar da ya yi da BBC kakakin ya ki bayyana yadda aka yi nasarar kubutar da mutanen biyu, illa dai ya ce sai a nan gaba ne za su yi wannan bayani.

Game da cewa ko an yi wani dauki-ba-dadi da wadanda suka sace jami’an ‘yan sandan biyu,

ganin yadda a cikin dan lokaci da sace su har aka yi nasarar ceto su,

musamman ma a yadda ake ganin masu satar jama’a na da makamai, sai ya danganta hakan da irin kokarin jami’an tsaro.

Hakkin mallakar hoto
Inpho

DSP Sabo ya ce ba a wannan lokacin ba ne kadai aka taba yin irin wannan nasara ta saurin ceto wasu da aka sace cikin gaggawa ba.

Ya ce abu ne da ya dogara da yanayin aiki, wani lokacin a samu nasara da wuri wani lokacin kuma yakan dauki lokaci.

Game da yadda ake ganin ‘yan bindiga na yawan satar mutane da kai hare-hare a jihar ta Kaduna,

a matsayin wata alama ta tabarbarewar tsaro a jihar, mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce abin ba haka yake ba, domin ba kasar da ba a aikata laifuka.

Ya ce sai dai kawai idan abu ya yi yawa yana tayar da hankalin mutane, wanda kuma rundunar ta yin duk abin da ya kamata domin maganin matsalar.

Ya kara da cewa sakamakon irin matakan da suke dauka a yanzu ba a yawan satar mutane a titin Kaduna zuwa Abuja, da sauran hare-hare da ake kai wa jama’a a jihar.

Ya ce yawanci ma a yanzu masu aikata irin wadannan laifuka sun koma wasu jihohi da ke makwabtaka da Kaduna ne, inda ya bayar da misalin iyakar jihar da Nasarawa ya ce a yanzu wasu a irin wadancan yankuna da ke da iyaka da Kaduna ake laifukan.

Sai dai ya ce akwai bukatar sauran jihohi masu makwabtaka da Kaduna su hada hannu domin maganin matsalar.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...