Jirgi mai saukar ungulu ya yi hatsari a Akwa Ibom

Wasu ma’aikatan kamfanin haƙar man fetur su 6 da kuma matuƙan jirgi su biyu su mutu a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a jihar Akwa Ibom.

Mutanen na kan hanyarsu ta zuwa a rijiyar mai ta OML 123 lokacin da jirgin ya faɗa cikin tekun Atlantika.

Bayanan da jaridar The Nation ta tattara sun nuna cewa mutanen sun nufi dandalin Mimbo wanda wani dandamali ne  kamar jirgin ruwa dake tsakiyar ruwa da ake haƙo ɗanyen mai a cikin teku tare da tara man kafin jiragen suzo su ɗauka.

Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:40 na safe.

Wata majiya ta shedawa jaridar ta The Nation cewa an gano gawarwakin mutane uku ayayin da ake cigaba da aikin gano ragowar mutanen.

Related Articles