Jiragen sojan saman Najeriya biyu sun yi hatsari a Abuja

Jirage biyu mallakin rundunar sojan saman Najeriya sun yi hatsari a Katampe wani gari dake kusa da Abuja.

Wata majiya ta shedawa jaridar The Cable cewa sun yi hatsarin ne lokacin da suke gwajin atisayen wasan jiragen sama da za a yi na bikin ranar mulkin kan Najeriya.

Ibikunle Daramola mai magana da yawun rundunar sojan saman Najeriya ya ce biyu matuka jirgin biyu sun samu nasarar fita daga ciki.

Ranar 17 ga watan Satumba rundunar sojan saman ta sanar da mazauna birnin tarayya Abuja cewa zata gudanar da atisayen gwaji inda ta ce mazauna birnin kada su firgita domin jiragen za su rika shawagi kasa-kasa.

More News

Mutane 21 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Lagos

Fasinjoji 21 ne suka rasa rayukansu bayan da wasu jiragen ruwa suka ci karo da juna a Imore dake karamar hukumar Amuwo-Odofin ta jihar...

Mutane 21 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Lagos

Fasinjoji 21 ne suka rasa rayukansu bayan da wasu jiragen ruwa suka ci karo da juna a Imore dake karamar hukumar Amuwo-Odofin ta jihar...

Ma’aikatan NAFDAC a Najeriya sun fara yajin aiki

Kungiyar Manyan Ma’aikata ta Kasa da Kamfanonin Gwamnati (SSASCGOC) reshen Kungiyar Kwadago ta Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta fara...

An ƙona sakatariyar ƙananan hukumomi 2 a jihar Rivers

Wasu da ake kyautata zaton ɓatagari ne sun ƙona wani sashe na sakatariyar ƙananan hukumomin Eleme da Ikwerre dake jihar Rivers. Ƙona ginin na zuwa...