Jiragen kamfanin Nigeria Air ya fara aiki

Rahotanni sun bayyana cewa wani jirgin kamfanin Nigeria Air, mai jigilar kayayyaki a Najeriya, ya kaddamar da tashinsa na farko zuwa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke babban birnin Najeriya, Abuja.

A halin yanzu dai jirgin ya bar birnin Addis Ababa na kasar Habasha, kuma ya isa birnin Abuja.

Tun da farko dai, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa alkawarin da kamfanin dillalan jiragen ya yi na fara aiki kafin wa’adin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kare a ranar 29 ga watan Mayu bai cika ba.

Sai dai a martanin da ya mayar kan rahoton, ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya tabbatar da cewa, kamfanin na Najeriya Air zai fara aiki a cikin wa’adin da aka kayyade.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...