Jinkirin ci gaba da shari’ar Ado Doguwa ba da gangan ba ne – Gwamnatin Kano


Gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani a kan zargin da wasu ‘yan fafutuka ke yi cewa ta Æ™i gurfanar da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai a gaban kotu.

‘Yan sanda sun kama Alhassan Ado Doguwa a Æ™arshen watan Fabarairu, inda suka kai shi kotun majistare bisa zargin ya harbi wasu mutane, kwana É—aya bayan zaÉ“en shugaban Æ™asa a mazaÉ“arsa ta Doguwa/Tudun wada.

Sun kuma tuhumi ɗan majalisar wakilan da kashe mutum uku, da raunata wasu takwas a ƙaramar hukumar Doguwa lokacin da ake karɓar sakamakon zaɓe.

Kotun dai, ta ba da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargin a gidan yari, kafin fara shari’a gadan-gadan.

Amma an ga shugaban masu rinjayen a cikin wani bidiyo da ya karaÉ—e shafukan sada zumunta kafin ‘yan sanda su kama shi, yana musanta zarge-zargen haddasa tashin hankali a lokacin zaÉ“en.

Sai dai, kwana É—aya kafin a mayar da shi kotun majistare, sai wata babbar kotun tarayya a Kano ta bayar da belin É—an siyasar ranar 6 ga watan Maris.

Tun daga lokacin kuma ba a sake jin batun komawa don ci gaba da shari’ar ba. Lamarin dai ya sa É“angarori da dama sun fara zargin ko hukumomi a Kano, na Æ™oÆ™arin danne maganar, har ta bi ruwa.

To amma a martanin da ta mayar ranar Laraba, ma’aikatar shari’ar jihar Kano ta ce ba da gangan, ta ƙi kai shi kotu ba.

A cewarta, jinkirin da aka samu wajen ci gaba da shari’ar, wani al’amari ne, na Æ™oÆ™arin bin tsari don tabbatar da adalci ga kowanne É“angare.

Kwamishinan shari’a na jihar Kano, Musa Abdullahi Lawan ya ce tun lokacin da aka fara gabatar musu batun Alhassan Ado Doguwa, suka lura cewa akwai kura-kurai.

”Don kuwa akwai wasu batutuwa da ba a shigar da su cikin takardun da suka shafi zarge-zargen da ake yi wa É—an siyasar ba,” in ji shi.

A cewar kwamishinan hakan zai iya kawo cikas a shari’ar, ko da an ci gaba da sauraren ta a kotu.

Gamayyar ƙungiyoyin fararen hular jihar Kano ne tun da farko, suka ce mutane da dama, ciki har da waɗanda rikicin na Tudun Wada lokacin zaben ya ritsa da su ne suke korafin cewa har yanzu gwamnati ta ƙi mayar da wanda ake zargin gaban kotu.

Ibrahim Wayya, shugaban gamayyar ya ce jikin mutanen da abin ya rutsa da su, ya fara yin sanyi saboda ganin take-taken kamar ba za a yi musu adalci ba.

Sai dai Musa Abdullahi Lawan, kwamishinan shari’a na jihar Kano ya ce ‘yan ƙungiyoyin ba su fahimci ina aka dosa game da zarge-zargen da ake yi wa Alhassan Ado Doguwa ba.

Abin da ya sa suke ganin kamar wani ne yake ƙoƙarin yin ƙafar-ungulu, zargin da kuma ba shi da tushe balle makama, a cewarsa.

Ina aka kwana game da binciken ‘yan sanda?

An tuntuɓi rundunar ’yan sandan Kano, don jin inda aka kwana game da binciken da suka ce sun faɗaɗa a kan zarge-zargen da ake yi wa ɗan siyasar, sai dai babu wani ƙwaƙƙwaran bayani da suka yi wa BBC zuwa yanzu.

Amma kwanan baya, an jiyo babban sufeton ‘yan sandan Najeriya yana umartar kwamishinoninsa na jihohi, su gaggauta kammala bincike a kan laifukan zaÉ“en da aka samu, don miÆ™a takardun bayanai ga hukumar zaÉ“e da nufin gurfanar da waÉ—anda ake zargi a gaban kotu nan take.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar 6 ga watan Maris, ta ce ‘yan sanda sun kama mutum 203 kan laifuka masu alaÆ™a da zaÉ“en shugaban Æ™asa da na ‘yan majalisun tarayya, baya ga bindigogi guda 18 a zaÉ“en na 25 ga watan Fabrairu.

Sanarwar dai ba ta yi Æ™arin bayani game da ko su wane ne mutanen da ‘yan sandan suka kama bisa zargi da aikata laifuka zaÉ“en ba.

Ita dai, hukumar zaÉ“en Najeriya ta ce ta yi maraba da matakin rundunar ‘yan sandan, na kammala bincike tare da damÆ™a mata takardun bayanan mutanen.

Ta ce tana zuba ido don karÉ“ar takardun, kuma cikin hanzari za ta kafa wani kwamiti na ayarin Æ™wararru a fannin shari’a don bin kadin zarge-zargen da ake yi wa mutanen, da gaske.

Zaɓen cike giɓi a Doguwa/Tudun wada

Tashe-tashen hankulan da suka faru a lokacin zaɓen ɗan majalisar tarayya na mazaɓar da Alhassan Ado Doguwa ke wakilta, sun sanya INEC ta ayyana zaɓen Doguwa da Tudun Wada a matsayin wanda bai kammala ba.

Da yake sanar da wannan matakin ranar Laraba 8 ga watan jiya na Maris , jami’in tattara sakamakon zaÉ“e, Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai ya ce tun da farko, ya yi shelar cewa É—an takarar na jam’iyyar APC ya lashe zaÉ“e ne, cikin tursasawa.

Ya ce an soke zaÉ“e a tashoshi 13 masu yawan mutanen da za su iya kaÉ—a Æ™uri’a 6, 917 a mazaÉ“ar Doguwa da Tudun Wada.

Sai dai daga bisani, bayan bita, hukumar zaÉ“e ta tabbatar cewa yawan Æ™uri’un da aka soke, sun zarce tazarar da ke tsakanin manyan ‘yan takara biyu a zaÉ“en.

A ranar Asabar 15 ga wannan wata na Afrilu ne, za a kammala zaÉ“en, inda a yanzu, shugaban masu rinjayen yake kan gaba da Æ™uri’a 39,732 a kan É—an takarar da ke rufa masa baya na jam’iyyar NNPP, da Æ™uri’a 34,798.

More News

Gwamnatin Adamawa Ta Ƙara Hutun Ɗaliban Makarantu Saboda Annobar Cutar Ƙyanda

Gwamnatin jihar Adamawa ta tsawaita lokacin komawar É—aliban jihar makarantunsu domin fara  zangon karatu na uku saboda annobar cutar Æ™yanda. A wata sanarwa ranar Litinin,...

Sojan Jamhuriyar Nijar sun kama Gawurtaccen ÆŠan Fashin dajin Najeriya Kachalla Mai Daji

Dakarun sojan Jamhuriyar Nijar sun samu nasara kama gawurtaccen É—an fashin dajin nan mai suna Kachalla Mai Daji a garin Illela dake kan iyakar...

Ƴan Fashin Daji Sun Kashe Mutane 7 A Jihar Kebbi

Mutane 7 aka bada rahoton ƴan fashin daji sun kashe  a garin Tudun Bici dake ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi. A cewar mazauna...

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraÉ—iyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...