10.3 C
London
Thursday, November 7, 2024
HomeHausaJinkirin ci gaba da shari'ar Ado Doguwa ba da gangan ba ne...

Jinkirin ci gaba da shari’ar Ado Doguwa ba da gangan ba ne – Gwamnatin Kano

Date:

Related stories

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...
spot_imgspot_img

Gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani a kan zargin da wasu ‘yan fafutuka ke yi cewa ta ƙi gurfanar da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai a gaban kotu.

‘Yan sanda sun kama Alhassan Ado Doguwa a ƙarshen watan Fabarairu, inda suka kai shi kotun majistare bisa zargin ya harbi wasu mutane, kwana ɗaya bayan zaɓen shugaban ƙasa a mazaɓarsa ta Doguwa/Tudun wada.

Sun kuma tuhumi ɗan majalisar wakilan da kashe mutum uku, da raunata wasu takwas a ƙaramar hukumar Doguwa lokacin da ake karɓar sakamakon zaɓe.

Kotun dai, ta ba da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargin a gidan yari, kafin fara shari’a gadan-gadan.

Amma an ga shugaban masu rinjayen a cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta kafin ‘yan sanda su kama shi, yana musanta zarge-zargen haddasa tashin hankali a lokacin zaɓen.

Sai dai, kwana ɗaya kafin a mayar da shi kotun majistare, sai wata babbar kotun tarayya a Kano ta bayar da belin ɗan siyasar ranar 6 ga watan Maris.

Tun daga lokacin kuma ba a sake jin batun komawa don ci gaba da shari’ar ba. Lamarin dai ya sa ɓangarori da dama sun fara zargin ko hukumomi a Kano, na ƙoƙarin danne maganar, har ta bi ruwa.

To amma a martanin da ta mayar ranar Laraba, ma’aikatar shari’ar jihar Kano ta ce ba da gangan, ta ƙi kai shi kotu ba.

A cewarta, jinkirin da aka samu wajen ci gaba da shari’ar, wani al’amari ne, na ƙoƙarin bin tsari don tabbatar da adalci ga kowanne ɓangare.

Kwamishinan shari’a na jihar Kano, Musa Abdullahi Lawan ya ce tun lokacin da aka fara gabatar musu batun Alhassan Ado Doguwa, suka lura cewa akwai kura-kurai.

”Don kuwa akwai wasu batutuwa da ba a shigar da su cikin takardun da suka shafi zarge-zargen da ake yi wa ɗan siyasar ba,” in ji shi.

A cewar kwamishinan hakan zai iya kawo cikas a shari’ar, ko da an ci gaba da sauraren ta a kotu.

Gamayyar ƙungiyoyin fararen hular jihar Kano ne tun da farko, suka ce mutane da dama, ciki har da waɗanda rikicin na Tudun Wada lokacin zaben ya ritsa da su ne suke korafin cewa har yanzu gwamnati ta ƙi mayar da wanda ake zargin gaban kotu.

Ibrahim Wayya, shugaban gamayyar ya ce jikin mutanen da abin ya rutsa da su, ya fara yin sanyi saboda ganin take-taken kamar ba za a yi musu adalci ba.

Sai dai Musa Abdullahi Lawan, kwamishinan shari’a na jihar Kano ya ce ‘yan ƙungiyoyin ba su fahimci ina aka dosa game da zarge-zargen da ake yi wa Alhassan Ado Doguwa ba.

Abin da ya sa suke ganin kamar wani ne yake ƙoƙarin yin ƙafar-ungulu, zargin da kuma ba shi da tushe balle makama, a cewarsa.

Ina aka kwana game da binciken ‘yan sanda?

An tuntuɓi rundunar ’yan sandan Kano, don jin inda aka kwana game da binciken da suka ce sun faɗaɗa a kan zarge-zargen da ake yi wa ɗan siyasar, sai dai babu wani ƙwaƙƙwaran bayani da suka yi wa BBC zuwa yanzu.

Amma kwanan baya, an jiyo babban sufeton ‘yan sandan Najeriya yana umartar kwamishinoninsa na jihohi, su gaggauta kammala bincike a kan laifukan zaɓen da aka samu, don miƙa takardun bayanai ga hukumar zaɓe da nufin gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu nan take.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar 6 ga watan Maris, ta ce ‘yan sanda sun kama mutum 203 kan laifuka masu alaƙa da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya, baya ga bindigogi guda 18 a zaɓen na 25 ga watan Fabrairu.

Sanarwar dai ba ta yi ƙarin bayani game da ko su wane ne mutanen da ‘yan sandan suka kama bisa zargi da aikata laifuka zaɓen ba.

Ita dai, hukumar zaɓen Najeriya ta ce ta yi maraba da matakin rundunar ‘yan sandan, na kammala bincike tare da damƙa mata takardun bayanan mutanen.

Ta ce tana zuba ido don karɓar takardun, kuma cikin hanzari za ta kafa wani kwamiti na ayarin ƙwararru a fannin shari’a don bin kadin zarge-zargen da ake yi wa mutanen, da gaske.

Zaɓen cike giɓi a Doguwa/Tudun wada

Tashe-tashen hankulan da suka faru a lokacin zaɓen ɗan majalisar tarayya na mazaɓar da Alhassan Ado Doguwa ke wakilta, sun sanya INEC ta ayyana zaɓen Doguwa da Tudun Wada a matsayin wanda bai kammala ba.

Da yake sanar da wannan matakin ranar Laraba 8 ga watan jiya na Maris , jami’in tattara sakamakon zaɓe, Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai ya ce tun da farko, ya yi shelar cewa ɗan takarar na jam’iyyar APC ya lashe zaɓe ne, cikin tursasawa.

Ya ce an soke zaɓe a tashoshi 13 masu yawan mutanen da za su iya kaɗa ƙuri’a 6, 917 a mazaɓar Doguwa da Tudun Wada.

Sai dai daga bisani, bayan bita, hukumar zaɓe ta tabbatar cewa yawan ƙuri’un da aka soke, sun zarce tazarar da ke tsakanin manyan ‘yan takara biyu a zaɓen.

A ranar Asabar 15 ga wannan wata na Afrilu ne, za a kammala zaɓen, inda a yanzu, shugaban masu rinjayen yake kan gaba da ƙuri’a 39,732 a kan ɗan takarar da ke rufa masa baya na jam’iyyar NNPP, da ƙuri’a 34,798.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories