Jam’iyun Habasha za su yi maja

Prime Minister Abiy Ahmed says the new party would help reduce ethnic divisions in Ethiopia

Hakkin mallakar hoto
Reuters

‘Yan siyasa a jam’iyya mai mulkin kasar Habasha ta People’s Revolutionary Democratic Front sun amince da wani shiri na kafa wata sabuwar jam’iyyar siyasa

Firai minista Abiy Ahmed ya fito yana mara wa wannan matakin na ‘yan siyasar baya.

Mista Abiy ya ce jam’iyyar da aka sanya wa suna Ethiopian Prosperity Party za ta taimaka wajen hada kan kabilun kasar wuri guda, kuma za ta hada kan ‘yan kasar.

Yana son sabuwar jam’iyyar ta zama wata hanya da za ta jagoranci siyasar kasar a madadin tsarin da aka shafe shekaru 30 ana bi na jam’iyyu masu alaka da manyan kabilun kasar.

Amma wani dan siyasa daa jam’iyyar Tigray People’s Liberation Front, jam’iyyar da ta mamaye siyasar kasar kafin zuwan Mista Abiy ya ce ba zai shiga sabuwar jam’iyyar ba.

Ya ce dalilinsa shi ne, shiga sabuwar jam’iyyar na iya dakushe karfin fada aji na bangaren siyasa da yake wakilta.

Firai minista Abiy ya aika da wani sako na Twitter, wanda a ciki ya ke cewa majar “wani muhimmin mataki ne a kokarinmu na hada karfinmu wuri guda domin cimma makomar da muke bukatar ganin kasarmu ta cimma.”

More News

Buhari ya rantsar da sabon Alkalin Alkalai

Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya rantsar da mai shari'a, Olukayode Ariwoola a matsayin, babban Alkalin Alkalai na Najeriya. Hakan na zuwa ne biyo bayan murabus...

‘Kyale kowa ya mallaki makami a Zamfara na da haɗari’

Masana a harkar tsaro sun bayyana cewa matakin da gwamnatin jihar Zamfara da ke Najeriya ta dauka na kyale farar-hula su mallaki bindiga yana...

Hotunan Daurin Auren Dan Gwamnan Nasarawa

Manyan baki da dama ne ciki har da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo suka halarci daurin auren dangidan gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule da...

Hotunan Daurin Auren Dan Gwamnan Nasarawa

Manyan baki da dama ne ciki har da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo suka halarci daurin auren dangidan gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule da...