Jami’ar Bayero ta samu lasisin bude gidan talabijin | BBC Hausa

Jami'ar Bayero ta yi fice wurin karantar da aikin jarida a Najeriya

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hukumar kula da kafafen yada labaru ta Najeriya, NBC, ta bai wa jami’ar Bayero da ke Kano lasisin da zai ba ta damar kafa gidan talabijin.

Wannan lasisi da jami’ar ta samu zai ba ta damar kafa gidan talabijin na kanta ta yadda za ta rinka koyar da dalibai aikin yada labaru na talabijin, a cewar shugaban hukumar ta NBC Ishaq Kawu.

Shugaban na NBC dai ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin jami’ar ta Bayero da ke Kano.

Yanzu haka dai jami’ar tana da gidan rediyo wanda ke yada labaru daga harabarta.

Shugaban bangaren karatun gaba da digiri na jami’ar Farfesa Umar Pate ya shaida wa BBC cewa sun samu tallafin kudaden gina dakin gabatar da shirye-shirye na gidan talabijin din daga wasu kungiyoyi.

Farfesan, wanda shi ne ya jagoranci sake gina gidan rediyon da samar masa da kayan aiki na zamani, ya ce nan gaba za a fara aiki domin gina gidan talabijin din.

Shugaban jami’ar Farfesa Muhammad Yahuza Bello ya ce wannan lasisi zai bunkasa harkar yada labaru a Najeriya.

Ya kara da cewa za a yi amfani da lasisin wajen horas da dalibai aikin jarida na binciken kwakwaf.

Jami’ar Bayero na daga cikin jami’o’in da suka yi fice a fannin koyar da aikin jarida a kasar.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...