Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 21 Da Aka Yi Garkuwa Dasu A Jihar Kogi

Jami’an tsaro a jihar Kogi sun samu nasarar ceto wasu mutane 21 sa’o’i 48 bayan anyi garkuwa da su.

Gwamna Yahaya Bello wanda ya yabawa kokarin jami’an tsaron ya jaddada cewa babu jihar baza ta amince da] masu aikata laifi.

A wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan kan kafafen yaɗa labarai Onogwu Muhammad ya fitar ta ce hadin gwiwar jami’an tsaron ƴan sanda, Civil Defence da kuma yan bijilante ne suka samu nasarar ceto mutanen.

Mutanen da aka ceto da yawancinsu matafiya ne anyi awon gaba da su ne a wajen wani daji mai sarkakiya dake karamar hukumar Ajaokuta ta jihar.

Muhammad ya ce samun labarin sace mutanen ke da wuya gwamna Bello ya bawa jami’an tsaro da kuma yan bijilante umarnin yin duk mai yiwuwa wajen ganin an ceto mutanen tare da kama wadanda suka yi garkuwat da su.

Wasu daga cikin masu garkuwar sun fada hannun jami’an tsaro a yayin da wasu suka tsere da raunin harbin bindiga kuma jami’an tsaron na cigaba da bibiyarsu.

More from this stream

Recomended