Jami’an tsaro sun ceto mutane 17 daga hannun yan bindiga ciki har da ɗan sanda

Rundunar tsaron haɗin gwiwa ta Operation Hadarin Daji dake kai ɗaukin gaggawa a yankin arewa maso yamma dake Malekachi a jihar Kebbi ta samu nasarar ceto wani ɗan sanda da kuma wasu mutane 16 daga hannun masu garkuwa da mutane.

Har ila yau rundunar ta samu nasarar kama babura da dama na yan bindigar a yayin da ta kai farmakin kuɓutar da mutanen.

Wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Yahaya Ibrahim a madadin jami’in yaɗa labarai na rundunar Operation Hadarin Daji ta ce sojojin sun hanzarta tattaruwa inda suka yi kwanton ɓauna a hanyar da suke tunanin yan bindigar za su wuce a ƙauyen Karenban.

Karfin wutar sojoji ne yasa yan bindigar suka tsere tare da barin mutanen da suke ɗauke da su.

“mutanen da aka ceto sun haɗa da mata 6 da kuma maza 11 ciki har da ɗan sanda da aka yi garkuwa da shi a Danko-Wasagu.” a cewar sanarwar.s

Sanarwar ta kara da cewa tuni aka miƙa wadanda aka ceto ga DPO yan sanda na Bena domin sada su da iyalinsu.

More News

Hukumar NMDPRA ta rufe wani gidan mai da ya karkatar da tankar man fetur 18

Hukumar NMDPRA dake lura da tacewa tare rarraba man fetur da iskar gas ta rufe gidan man Botoson Oil and Gas LTD dake jihar...

Jirgin saman kamfanin Xejet ya zame daga kan titin filin jirgin saman Lagos

A ranar Asabar ne wani jirgin sama mallakin kamfanin Xejet ya zame daga kan titin filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos. Hukumar NSIB dake...

Lauya ya nemi kotu ta bashi mako 4 ya nemo inda Yahaya Bello ya ɓuya

Abdulwahab Mohammed babban lauyan tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya nemi babbar kotun tarayya dake Abuja da ta bashi makonni huɗu domin ya...

Ɗalibai 9 aka tabbatar da yin garkuwa da su daga jami’an jihar Kogi

Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da cewa ɗalibai 9 aka tabbatar sun ɓace bayan da wasu ƴan bindiga suka kai farmaki Jami'ar Kimiya da...