Jami’an Hukumar EFCC Sun Ziyarci Hedkwatar Rukunin Kamfanonin Dangote

Jami’an hukumar EFCC dake yaki da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ta’annati sun ziyarci hedkwatar rukunin kamfanonin Dangote a jihar Lagos a yayin da hukumar ta EFCC ke faÉ—aÉ—a bincike kan batun zargin badakalar musayar kudaden waje a lokacin, Godwin Emefiele tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN.

Idan za a iya tunawa a cikin watan Nuwamba ne Rukunin Kamfanonin Dangote ya musalta zargin cewa ya aikata ha’inci da kuma almundahanar kudade har na kusan dala biliyan 3.4.

Amma kuma ranar Alhamis hukumar EFCC ta bukaci kamfanin ya bata takardun bayanai dake da alaka da batun bawa kamfanin musayar kudaden kasar waje tun daga shekarar 2015 har ya zuwa lokacin da shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da Emefiele daga kan muƙaminsa.

Wasu daga cikin ma’aikatan kamfanin sun tabbatarwa da jaridar Daily Trust cewa lallai jami’an hukumar ta EFCC sun ziyarci kamfanin.

Binciken na hukumar EFCC ba iya kamfanin Dangote ya tsaya ba ya hada da wasu manyan kamfanoni da suma suka samu musayar kudaden waje a farashin gwamnati a hannun CBN har ya zuwa shekarar 2023.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...