
Hukumar Kula Da Shige Da Fice ta Najeriya ta ce jami’anta huɗu sun mutu a yayin da wasu 7 kuma suka samu rauni a wani hatsarin mota akan hanyar Kano-Zaria.
Hatsarin ya faru ne ƴan kilomitoci kaɗan daga birnin Kano.
Mai magana da yawun hukumar, Adedotun Aridegbe shi ne ya sanar da faruwar lamarin a wurin wani taron manema labarai ranar Litinin a Abuja.
Aridegbe ya ce ma’aikatan na kan hanyarsu ne ta komawa Abuja daga wani aiki da aka tura su a Kano a lokacin da lamarin ya faru.
Ya kara da cewa awadanda suka samu rauni a hatsarin na samun kulawa a Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano dake Kano.