Iyaye na kokawa kan ƙarin kuɗin makaranta a wasu jami’o’in Najeriya—BBC

Iyaye a Najeriya sun fara kokawa da ƙarin kuɗin makaranta da wasu jami’oin Najeriya suka yi, yayin da bayanai ke cewa wasu kuma na shirin yi.

Ƙungiyar ɗaliban jami’o’in kasar ta ce ba za ta saɓu ba.

Sanarwar da wasu jami’o’in Najeriya suka fitar na cewa daga zangon karatu na gaba an kara kuɗin makaranta, wanda hakan ya yi matuƙar tayar da hankalin wasu daga cikin iyaye da ɗalibai, saboda a cewarsu da ma da kyar suke biyan kuɗin makarantar na yanzu.

Wani mahaifi, Saifullahi Danhassan ya ce ƴarsa ta kawo masa sanarwa daga jami’ar tarayya ta Dutse, cewar an ƙara kuɗin makaranta.

“Da wanne za mu ji? Abinci na neman ya fi ƙarfin mutane, sannan ga shi ana cewar ilimin nan shi ne gatan al’umma, ya kamata gwamnati ta yi gyara, domin da alama da yawa daga cikin iyaye ba za mu iya biyan kuɗin da aka ƙara ba, kuma ko da za mu iya, ƙalilian ne daga cikin mu za su iya, ya kamata dai gwamnati ta duba.”

Haka zalika ita ma wata uwa, ta ce “ƴaƴan talakawa ba za su iya ilimi ba idan ma za su iya sai an yi kararuma sannan za su yi, wanda bayan kuɗin makarantar ma ba a maganar abin da za su ci da abin da zai taso a makarantar, yaya aka iya yanzu ma bare a ce an yi wannan ƙarin wanda ba a san me zai zo a gaba ba?”

Me ASSU ke cewa kan ƙarin kuɗin makarantar?

Ƙungiyar malaman jami’oin Najeriya ta ASUU ta ce da ma ta san za a rina, saboda kuɗaɗen gudanarwa da jami’o’in suke karɓa daga gwamnatin tarayya ba su isa.

Farfesa Abdulkadir Muhammad shi ne shugaban ASUU na jihar Kano ya shaida wa BBC cewar “irin wannan ƙarin za ka ga ya tafi yaro zai ringa biyan naira 200, 000 zuwa 250, 000, to yayin da aka ce gwamnati ta janye hannunta daga yadda ake tafiyar da jami’o’in Najeirya, za ka ga ɗalibi zai biya ya fi ƙarfin naira 200, 000 sai ya kai naira 700, 000, ko sama da haka.

“Ko yajin aikin da muka yi na wata takwas da waɗanda muka yi a baya, mun yi su ne don matsa wa gwamanti ta kawo kuɗaɗen da za a rinƙa tafiyar da jami’o’in nan, amma gwamnati ta ƙi.”

Ƙarin labarai

Farfesa Abdulkadir Muhamamd ya ƙara da cewar kamar yadda shugaban Najeriya Muhamamdu Buhari ya faɗa a kwanakin baya, ‘gwamnati ba za ta iya ci gaba da ɗaukar nauyin tafiyar da jami’o’in ƙasar ba, sai tare da haɗin gwiwar iyayen ɗalibai’, wanda ƙarin shi ne abin da aka fara gani.

Bayanai na cewa tuni wasu jami’oin suka ƙara kuɗin makarantar da fiye da kashi ɗari, inda ƙarin zai fara aiki a zangon karatu na gaba, sannan wasu da dama ciki har da jami’ar tarayya da ke Dutsen jihar JIgawa suke kan tattauna yadda za su yi ƙarin.

More News

Ƴan Fashin Daji Sun Kashe Mutane 7 A Jihar Kebbi

Mutane 7 aka bada rahoton ƴan fashin daji sun kashe  a garin Tudun Bici dake ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi. A cewar mazauna...

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraɗiyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...