Isra’ila za ta dinga leken asiri kan wayoyin masu coronavirus

Benjamin Netenyahu puts a figner in his ear while listening intently to a phone call

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Gwamnatin Israila ta amince da saka matakan gaggawa na leken asiri a wayoyin mutanen kasar da za su bi diddigin masu dauke da coronavirus.

Za a yi amfani da sabbin matakan wajen killacewa da kuma gargadin wadanda suka yi mu’amula da masu dauke da cutar.

An amince da matakan na wucin gadi yayin wani zaman dare daya da majalisar zartarwar kasar ta yi.

Majalisar zartarwar kasar ba ta ko nemi amincewar majalisar dokokin Isra’ila ba kafin ta dauki wannan mataki.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta kasar ta kira wannan lamari mummunar hanya da gwamnatin ta dauka da baza ta bulle ba.

Wadannan matakan ana daukar su ne kawai domin dakile harin ta’addanci.

Ba a bayar da bayanai dangane da yadda za a yi amfani da intanet wajen bin diddigin ba, amma ana ganin cewa idan aka tattara bayanan daga wurin da mutum yake, za a tura su zuwa wajen ma’aikatan lafiya.

Da zarar an samu labarin ana zargin mutum na dauke da coronavirus, ma’aikatar lafiyar za ta iya bin diddigin ko mutum na bin dokokin killacewa ko ba ya bi.

Za kuma a iya tura sako ga mutanen da suka yi mu’amula da su kafin alamomin cutar su fara nunawa.

Isra’ila ta tabbatar da mutum 300 na dauke da coronavirus kuma ta sanya matakai daban-daban domin dakile bazuwar cutar.

Matakan sun hada da kulle makarantu da shaguna da wuraren cin abinci da na shakatawa da kuma takaita taro zuwa mutum 10.

Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa wannan matakin da aka dauka na leken asiri a wayoyi da bin diddigi zai dauki kwanaki 30 ne kacal.

More News

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...