Ipman ta shaida dalilin da ya sa wahalar man fetur ta sake kunno kai a Najeriya

Kungiyar manyan dillalan man fetur ta kasa a Najeriya ta yi barazanar dakatar da siyar da man fetur a faɗin ƙasar, har sai hukumar da ke daidaita farashin man fetur ta kasa ta biyata kuɗaɗenta da mambobinta su ke bin gwamnati.

Kungiyar ta IPMAN ta ce kimanin wata 9 kenan da hukumar ta yi burus da su, ba ta biyansu kuɗaɗensu da yawan su ya kai aƙalla naira biliyan dari 500.

Shugaban Kungiyar dillalan man reshen arewacin Najeriya, Bashir Ahmed Dan Malam ya shaidawa BBC cewa wannan ne ya sa mambobinsu su ka janye daga dakon man fetur abinda ya haifar da dogayen layukan mai da aka soma gani a birnin tarayya Abuja da kuma wasu jihohin ƙasar.

Ya kuma yi gargadin cewa matsalar za ta yi kamari idan hukumar ba ta dauki matakin biyansu ba.

“Tura ta riga ta kai bango mutane da suna iya zuwa su dauko wadannan kaya amma ta kai mutane yanzu…duk wanda ya je ba iya komawa, wasu sun sayar da gidajen man ma, wasu sun kar-karye, wasu sun mutu da bakin cikin rashin biya a cikin wannan harkar ta dakon mai,” in ji Dan-Mallam.

‘Za a ji jiki idan ba a biya mu ba’

Kungiyar ta IPMAN ta yi zargin cewa tun da aka kafa sabuwar hukumar da ke sa ido a kan albarkatun man fetur sau biyu kawai ta biyasu kuɗaɗensu kuma tun bayan wannan lokaci ba ta kara biyansu ba.

A cewar Bashir Dan Malam matsalar ta fi shafar dillalan man fetur na yankin arewacin ƙasar.

“Duk man da za mu saya akwai inda aka sa naira 7 da digo 5 a kan kowace lita wadda ake sakawa a cikin template dinnan, toh wadannan kuɗaɗe su ne ake tattarawa ake ba mu to amma mu mutanen arewa, mu muka fi shan wahala saboda wannan harka ta ba fita kuma komai ya tsaya.”

“Mu ba maganar kari mu ke bukata ba, mu abinda muke so shi ne a biyamu kuɗaɗenmu , mu cigaba da harkokinmu,” in ji shi.

Sai dai duk da cewa tuni ‘yan Najeriya suka fara jin jiki sakamakon karancin man fetur da ake fuskanta a kasar, IPMAN ta ce bisa la’akari da haka ne ta kira taron ‘yan jarida inda ta yi kira ga gwamnati domin ta sa baki a cikin al’amarin kafin ya kara yin muni.

IPMAN ta ce muddin aka biya waɗannan kuɗaɗe to za a daina ganin layukan motocin a gidajen man fetur.

Najeriya kasa ce mai arzikin man fetur sai dai kusan kowanne lokaci ta na yawan fuskantar matsalar man fetur.

Ko a baya kasar ta sahafe kusan watanni uku tana fama da karancin mai abinda ya haifar dogayen layukan mai a gidajen mai.

Irin waɗannan matsaloli na taka rawa wajen sake dukushewar tattalin arzikinta da safe ta’azzara tsadar rayuwa.

More from this stream

Recomended