INEC za ta gudanar da zaben gwamnonin Kogi da Bayelsa

Farfesa Mahmoud
Image caption

Tun da fari INEC ta sanya watan Nuwamba mai zuwa a matsayin lokacin zaben gwamnonin jihohin Kogi da Bayelsa

A Najeriya hukumar zabe mai zaman kan ta, ta sanya lokacin da za a gudanar da zaben gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da INEC ta aike wa manema labarai.

A ranar tara ga watan Afirilu da ya wuce ne INEC ta fitar da jadawalin yadda zaben zai kasance a ranar biyu ga watan Nuwamba mai zuwa.

Daga bisani hukumar ta yi ta samun kiraye-kiraye daga gwamnati, da majalisu da shugabannin al’umma har da na addinai daga jihar Bayelsa kan a sauya lokacin saboda ya zo dai-dai da ranar addu’ar shekara-shekara da ake gudanarwa tun daga shekarar 2012.

Bayan nazari da tuntubar juna, hukumar zaben ta sanar da ranar Asabar 16 ga watan nan a matsayin ranar da za a gudanar da zaben gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa.

More from this stream

Recomended