Illolin da magungunan taƙaita haihuwa suke yi wa mata

  • Daga Sandrine Lungumbu
  • BBC World Service
Bayanan hoto,
Vanessa Centeno: ‘We always think it will never happen to me, but it did.’

A lokacin Vanessa Centeno akwai wani gudan jini a huhunta, ta shiga wani hali.

Amma da ta fahimci abin da ya janyo mata gudan jinin, sai ta dimauce.

A 201, ma’aikaciyar da ke zaune a birnin Boston, kamar sauran miliyoyin mata a fadin duniya, na shan kwayoyin barin tazara tsakanin haihuwa.

Amma ba kamar sauran matan ba, Vanessa ta fuskanci wata illa da ke tattare da amfani da irin wadannan magungunan – gudan jinni, wanda ta ce ya sauya rayuwarta har abada.

‘Na dauka bugun zuciya na samu’

“Ina hawa bene sai kawai na ji numfashina ya dauke,” a cewar Vanessa.

“Ban taba jin irin haka ba sai na yi kokarin jan numfashi sosai.”

Duk da halin da ta tsinci kanta Vanessa ta je aiki amma ta tashi da wuri don ta je asibiti.

“Sun ba ni wata na’ura da za ta taimaka wajen bude hanyoyin iska a jikina.

“Na dan ji sauki kuma numfashin ya daina yi min wahala. Sun dauki hoton huhuna sai suka ce sun ga wata inuwa a ciki babu mamaki limoniya ce.”

Amma washegari sai asibitin suka sanar da Vanessa cewa ba limoniya ba ce amma za su sake yi mata gwaje gwaje.

Sai da aka kwashe wata guda ba ta samu ganin likita ba, ga shi numfashi na kara yi mata wahalar yi.

“Rannan ina aiki a gida, ina wanke kayana ina ta hawa da sauka a bene sai numfashina ya fara daukewa, sai na zuge zif din rigata. Nan na fadi kasa a dakin girki saboda na kasa shakar iska.

“Jikina babu inda ba ya ciwo, cikina, kirjina da hannuwana duk suka rika ciwo. Na dauka bugun zuciya zan samu.”

Vanessa ba ta je asibiti ba amma ta buga wa likitanta waya, inda aka ba ta shawarar ta je asibitin cikin gaggawa.

“Washe gari, na je na ga likita na gaya mata yadda nake ji sai ta duba ni. Daga nan ne ta tura ni babban asibiti don a yi min gwaje gwaje sosai.

“Na je aka jona ni a jikin na’urori, gaba daya na shiga rudani.”

“An gano ashe ina da wani katon gudan jini a kirjina, kuma ya fara farfashewa har mamaye mafi yawan huhuna.”

Kwanan Vanessa biyu a asibiti kafin a sallame ta amma mako biyu ta kwashe tana jinya.

Ta ce likitoci sun gaya mata mai yiwuwa sauya kwayoyin hana daukar ciki da ta yi ne ya janyo mata wannan gudan jinin.

“An shaida min cewa da na kara kwana guda kafin in zo asibiti da na rasa rayuwata,” a cewarta.

Dama ana yawan samun gudan jini a mata masu shan kwayoyin takaita haihuwa?

Bayanan hoto,
The pill is the most common form of contraception in Europe, Australia and New Zealand

A cewar Hukumar Insorar Lafiya ta Burtaniya NHS, a kasar, ‘ya danganta tsakanin mata biyar zuwa 2 ne ke samun gudan jini a cikin mata 10,000 da ke amfani da su a shekara.

NHS ta ba da shawarar cewa duk macen da ke cikin shakku ta tuntubi likitanta.

A fadin duniya, mata sama da miliyan 150 ne ke shan wadannan magungunan kuma su ne suka fi shahara a Turai da Australia da New Zealand. Kuma su ne na biyu mafiya shahara a Afrika da Latin Amurka da Amurka.

Kwayoyin, kamar ko wane nau’i na tazarar haihuwa na da illolinsu ciki har da yawan fushi da sa kiba ko rama. Wadannan ne aka fi gani.

Amma akwai illolin da ba a cika gani ba kamar samuwar gudan jini wanda ke da hadari. Wannan hadarin ya danganta ne da yawan sindarin da mace ke samu daga kwayoyin da shekarunta da yadda take gudanar da rayuwarta misali idan mai kiba ce ko kuma idan tana shan taba sigari.

Ba kowa ne ke samun gudan jini ba

Kwayoyin na da sindarin oestrogen da aka samar a dakin gwaji ko progesterone ko duka biyun.

“Sinadarin Oestrogen na janyo samuwar kwayaye a mahaifa, don haka idan kwayayen suka yi kwari sai su sakko zuwa mahaifa inda a nan ne ciki zai iya samuwa, a cewar Dakta Zozo, kwararriya a bangaren haihuwa a asibitin Steve Biko da ke Pretoria a Afrika ta Kudu.

“Amma idan sinadarin oestrogen ya yi yawa sai ya bai wa kwakwalwa alamar haka, sai a samar da kwayaye,” a cewarta.

Dakta Nene ta yi bayanin cewa sinadarin progesterone na aiki ta hanyoyi uku ne; yana kara kaurin ruwan da ke bakin mahaifa don kada maniyyi ya samu damar wucewa.

Sannan yana hana mahaifa rike jariri.

Haka kuma, yana tunkudo kwai ya biyo hanyoyin nan da ake kira “fallopian tubes” ya hadu da maniyyi a samar da jariri.

“Don haka sinadaren biyu na aiki tare don hana samar da kwayaye da kuma zaman jariri a mahaifa,” a cewarta.

Illolin shan wadannan kwayoyin da ake gani sun hada da tashin zuciya da amai da kara kiba da kumburin ciki da kuraje a fuska.

“Wasu kan ce sun samu raguwar sha’awa da ciwon kai da jin zafi a mamansu da yawan fushi,” in ji Dakta Nene.

“Yana da kyau a san abin da ke jawo wadannan illoli ,” in ji ta.

Jikin dan Adam na da sindaran da ke iya samar da gudan jini dai dai wa dai da. Amma idan suka hadu da irin wadannan kwayoyin sai hatsarin samun gudan jinni ya karu a jiki.

Bayanan hoto,
Vanessa has tried different forms of contraception over the years including an implant

‘Na gamu da tabin hankali na PTSD’

Sama da shekara guda bayan Vanessa ta fuskanci wannan ibtila’i, ta kasa ci gaba da rayuwarta yadda ta saba.

“Lokaci guda na gamu da wannan matsala kuma sai da na sha magunguna tsawon wata shidda.

“Na gamu da tabin hankalin na PTSD wanda ke faruwa idan mutum ya fuskanci wani abin tashin hankali.

“Da zarar na fara wanke kayana sai in ji abin ya dawo min sabo, saboda matsalar ta taso min ne ranar ina tsaka da wanke kaya,” a cewarta.

“Sai na kan tuna wa kaina yanzu na samu lafiya kuma ba na cikin hadari.”

“Ban san abin da ya janyo min wannan matsala ba saboda na dade ina shan wadannan kwayoyin a baya.”

Akwai dalilai da dama da ke sa mata shan kwayoyin hana daukar ciki, amma mafi yawan lokuta lamarin na kudi ne.

Vanessa ta yi aiki a matsayin ‘yar kwangila a kusa da Boston, don haka sai ta je asibiti aka sa mata wani tsinke a hannunta wanda shi ma yana iya hana daukar ciki har sai ta samu aiki na din din din.

“Tsinken na da alfanu amma sai na kula yana sa ni kiba. Sai na je aka cire shin a fara shan kwayoyin”

“Ina ga mun riga mun saba da jin cewa wadannan magungunan na iya janyo mana wasu illoli ko ma mutuwa.”

Gani mu ke ba zai iya faruwa da mu ba, amma ya faru da ni kuma ya sauya min rayuwa sosai.”

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa ɗaya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faɗa tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...