Hukumar ta ce kamfanin ya gawurta domin har yana fitar da A-kuskura zuwa kasashen Chadi da Kamaru da Jamhuriyyar Nijar.
A kwanakin baya ne NDLEA ta yi gargadi kan amfani da A-kuskura. Photo/NDLEA
Hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyin a Nijeriya NDLEA ta ce ta gano wani kamfani da ake hada A-kuskura a garin Mubi na Jihar Adamawa.
Hukumar ta ce kamfanin ya gawurta domin har yana fitar da A-kuskura zuwa kasashen Chadi da Kamaru da Jamhuriyyar Nijar.
Mai magana da yawun hukumar ta NDLEA Femi Babafemi ne ya sanar da batun kamun a wata sanarwa da ya fitar mai kunshe da bayanai kan kamen da suka yi na miyagun kwayoyi.
Babafemi ya bayyana cewa a lokacin da da aka kai samamen, ana cikin aikin hada A-kuskura.
A-kuskura dai wani hadi ne ko kuma jiko da ke sa mutum maye ko kuma ya fita daga cikin hayyacinsa musamman a karon farko da aka soma amfani da shi.