Hukumar DSS tal gurfanar da Emefiele a gaban kotu

Hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS ta ce ta gurfanar da tsohon shugaban Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele a gaban kotu.

Hukumar ta sanar da haka ne a matsayin wani martani da umarnin da babbar kotun birnin tarayya dake cewa a saki Emefiele cikin kwana bakwai ko kuma a gurfanar da shi a gaban kotu.

Alkalin kotun mai shari’a Hamza Mu’azu shi ne ya yanke hukuncin kan kara da Emefiele ya shigar na tauye masa hankinsa na dan adam.

Kakakin hukumar ta DSS, Peter Afunaya a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce tuni hukumar ta bi umarnin kotun ta hanyar gurfanar da Emefiele a gaban kotu.

Afunaya ya tabbatarwa da jama’a cewa hukumar za ta cigaba da nuna kwarewa, adalci da kuma dai-daito a wajen binciken tare da yin ayyukanta bisa bin doka.

More from this stream

Recomended