Gwamonin APC 9 Na Son Mulki Ya Koma Yankin Kudu

Wasu gwamnonin arewa 9 na goyon bayan jam’iyar APC ta tsayar da dantakarar shugaban kasa daga yankin kudu.

A mako mai zuwa ne dai jam’iyar ta APC za ta gudanar da zaben fidda gwanin dantakarar shugaban kasa inda aka tantance yan takara 23 da ake sa ran za su fafata a zaben.

Tuni wasu ke kokarin ganin dantakarar jam’iyar ya fito daga arewa bayan da jam’iyar PDP ta zabi Atiku Abubakar a matsayin wanda zai mata takara. Masu wannan kokarin na ganin cewa fitar da dantakara daga arewa ne kadai zai bawa jam’iyar APC nasara a zaben 2023.

Sai dai gwamnoni irinsu, Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, Babagana Umara Zulum na jihar Borno, Simon Lalong na jihar Filato, Abubakar Sani Bello na jihar Niger, Aminu Masari na jihar Katsina, Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, Bello Matawalle na jihar Zamfara da kuma Abdulrahman Abdulrazak na jihar Kwara na ganin cewa yin haka ba dai-dai bane kuma ya saba da yarjejeniyar mutuntaka da aka cimma a baya na cewa mulki zai koma kudu bayan shugaba Buhari ya kammala mulkinsa.

Duk da cewa ra’ayin gwamnonin ya zo daya kan yankin da dantakarar zai fito ra’ayin su ya sha banban kan mutumin da ya kamata jam’iyar ta tsayar takara daga yankin kudu.

More from this stream

Recomended