
Wata tawagar kungiyar gwamnonin Najeriya sun kaiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ziyara a birnin Lagos.
Da yammacin ranar Alhamis ne Tinubu ya isa Lagos daga Abuja cikin jirgin shugaban ƙasa inda ya sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Ikeja.
Shugaban kasar ya samu tarba daga gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu da kuma dumbin tarin magoya baya.
A ranar Talata wani fefan bidiyo ya bayyana inda aka ga gwamnonin karkashin jagorancin gwamnan jihar Kwara, Abdulrahaman Abdulrazak suna shiga motar safa da za ta kai su gidan shugaban kasar.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila na daga cikin wadanda da suke nan a lokacin ziyarar.