Gwamnan Zamfara ya gargadi masu neman tayar da zaune tsaye

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle

Image caption

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Mohammed

Gwamnan jihar Zamfara Bello Mohammed ya sanar da cewa gwamnatin jihar na da bayanan sirri da suka tabbatar ma ta cewa wasu ‘yan siyasa na kokarin tayar da zaune tsaye tsakanin al’umomin jihar.

Gwamnan ya kuma ce ‘yan siyasan, wadanda ya kira marasa kishin kasa na yin yunkurin ne ta karkashin kasa domin cimma burinsu na siyasa kawai.

Ya zarge su da hada kai da wasu ‘yan kungiyar Boko Haram da aka fatattaka daga yankin Arewa maso gabas domin kai hare-hare kan mutanen da basu san hawa ba, basu san sauka ba.

Kuma ya ce dalilinsu na daukan wannan matakin shi ne don su tarwatsa zaman lafiyar da ke wanzuwa cikin jihar da kuma lalata shirin sulhu da gwamnatin da yake jagoranta ta samar.

Amma gwamnan bai bayyana sunayen ‘yan siyasan da yake tuhuma da shirya wannan aika-aikar ba, kuma kawo yanzu, BBC ba ta da hanyar tabbatar da sahihancin sanarwar.

Sanarwar da gwamnan ya fitar ta hannun Yusuf Idris Gusau, wanda shi ne mataimakinsa na musamman kan hulda da kafofin yada labarai, ta bayyana yadda aka shirya kai hare-hare cikin jihar.

Sanarwar ta ce akwai shirin kai hare-hare cikin kananan hukumomi bakwai na jihar ta Zamfara, bayan wasu muhimman wurare a babban birnin jihar na Gusau.

Cikin shirin da gwamnan ya ce sun bankado, akwai wani da aka kitsa domin hallaka wasu fitattu da sanannun ‘yan asalin jihar.

BBC ta ga sanarwar da gwamnan ya fitar, inda a ciki ya bayyana sunayen kananan hukumomin da ya ce a shiry akai hare-hare:

Akwai Gusau, wanda shi ne babban birnin jihar, da Tsafe da Talata Mafara da kuma Anka.

Sauran kananan hukumomin da ka ambato sun hada da Zurmi da Maru da kuma Maradun, kuma sanarwar ta ce an shiry akai hari kan babban masallacin Gusau da kasuwar Mammy Market.

Hakkin mallakar hoto
Zamfara State Government

Sannan sanarwar ta ce ‘yan kungiyar Boko Haram aka shirya za su kai wadannan hare-haren ne daga Litinin 23 ga watan Satumba zuwa 25 ga watan na Satumba, shekarar 2019.

Gwamnan Bello Mohammed ya tabbatar wa al;umomin jihar cewa gwamnati za ta dauki dukkan matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyinsu.

Hakkin mallakar hoto
@BELLOMATAWALLE1

Image caption

Gwamna Bello Mohammed da Shugaba Muhamamdu Buhari

A wani labari mai alaka da wannan, gwamantin jihar Zamfara ta bayyana gamsuwarta da sakin wasu mutum 30 da a baya masu satar mutane domin karban kudin fansa ke tsare da su.

Wadanda aka sakin sun hada da mata 15 da maza 15, wadanda dukkansu ‘yan asalin karamar hukumar Kaura Namoda ne, kuma sun shafe wata takwas a hannun barayin gabanin sakin nasu da aka yi.

More News

Peter Obi Ya Ziyarci Mutanen Da Su Ka Ƙone Sakamakon Wutar Da Wani Ya Cinnawa   Masallaci A Kano

ÆŠan takarar shugaban Æ™asa  a zaÉ“en 2023 Æ™arÆ™ashin jam'iyar Labour Party (LP) Peter Obi ya ziyarci mutanen da wani matashi ya cinnawa wuta a...

An sanar da zaman makoki na kwana biyar saboda mutuwar shugaban kasa a Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya sanar da zaman makoki na kwanaki biyar saboda rasuwar shugaban kasar Ibrahim Raisi...

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...