Gwamnatin tarayya ta dakatar da karɓar harajin VAT kan man Diesel

Gwamnatin tarayya ta ce zata jingine batun karbar harajin VAT kan man Diesel har sai bayan nan da wata shida a wani mataki na rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Hakan na cikin matsayar da aka cimma tsakanin gwamnatin tarayya da yan kungiyoyin ƙwadago ta NLC da TUC da gwamnatin a taron da suka yi jiya.

Da yake magana a karshen taron ganawar da aka yi shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya ce gwamnatin da kungiyar ƙwadago sun cimma wasu matsayoyi.

Sai dai wasu masana na ganin ya kamata gwamnati ta dauki matakai na dindindin domin magance tsadar rayuwa da yan Najeriya ke fama da ita.

More News

Ƴan Fashin Daji Sun Kashe Mutane 7 A Jihar Kebbi

Mutane 7 aka bada rahoton ƴan fashin daji sun kashe  a garin Tudun Bici dake ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi. A cewar mazauna...

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraɗiyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...